Jerin Manyan Yan Siyasar Najeriya 10 da Aka Haifa a Watar Disamba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Watar Disamba wata ce ta musamman ta bangarori da dama. Baya ga kasancewarta watar karshen shekara, tana ba mutane daman waiwayon yadda rayuwarsu ta kasance a shekara. Wasu kuma kan samu damar yin bikin zagayowar ranar haihuwarsu a cikin watar.
Ranar haihuwar fitattun yan Najeriya da dama ya fada a cikin wannan wata ta Disamba.
A wannan zaure, Legit Hausa ta tattaro jerin yan siyasar Najeriya da aka haifa a cikin wannan wata ta Disamba.
1) Muhammadu Buhari
Buhari wanda ya kasance haifaffen dan Daura, jihar Katsina shine tsohon shugaban kasar Najeriya da ya mika mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kasa daga 2015 zuwa 2023 zai cika shekaru 81 a ranar 17 ga watar Disamba. Ya kasance Manjo Janar mai ritaya, ya yi shugaban mulkin soji daga 1983 zuwa 1985, bayan ya karbi mulki ta juyin mulkin soja.
2) Godswill Akpabio
Sanata Akpabio shine shugaban majalisar dattawan Najeriya mai ci. Shine sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a majalisar dokokin tarayya. Ya yi aiki a matsayin ministan harkokin Neja Delta daga 2019 zuwa 2022.
Ya kuma yi gwamnan jihar Akwa Ibom daga 2007 zuwa 2015. An haife shi a ranar 9 ga watar Disamba, 1962.
3) Seyi Makinde
An haifi Injiniya Makinde, a ranar Kirsimeti wato 25 ga watar Disamba, 1967, Shine gwamnan jihar Oyo mai ci a yanzu.
4) Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje mai shekaru 73 a duniya, shine tsohon gwamnan jihar Kano, inda ya yi shugabanci sau biyu. Ya kuma rike mukamin mataimakin gwamna sau biyu daga 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.
Shine shugaban jam'iyyar APC na kasa mai ci a yanzu. An haifi Ganduje a ranar 25 ga watar Disamba.
5) Bukola Saraki
Saraki ya yi aiki a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 13 daga 2015 zuwa 2019. Ya kuma yi gwamnan jihar Kwara daga 2003 zuwa 2011.
An haifi Saraki wanda ke da shekaru 60 a yanzu haka a ranar 19 ga watan Disamba.
6) George Akume
Akume, wanda aka haifa a ranar 27 ga watan Disamba shine sakataren gwamnatin tarayya mai ci a yanzu haka.
Ya yi aiki a matsayin ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati karkashin mulkin Buhari. Akume ya kuma kasance tsohon gwamnan jihar Benue.
7) Abdulfatah Ahmed
Ahmed wanda aka haifa a ranar 29 ga watar Disamba, 1963 shine tsohon gwamnan jihar Kwara wanda ya mika mulki.
Dan siyasar wanda ya kasance ma'aikacin banki ya bar karagar mulki a 2019.
8) Lai Mohammed
An haifi tsohon ministan labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed a ranar 6 ga watar Disamba, 1951. Ya kasance tsohon sakataren labarai na jam'iyyar APC na kasa.
Kamar dai Saraki da Ahmed, Mohammed ma shahararren dan siyasa ne daga jihar Kwara.
9) Yakubu Dogara
Dogara wanda ya kasance hafaffen dan jihar Bauchi ya yi aiki a matsayin kakakin majalisar wakilai ta 13.
An haifi Dogara wanda ya kasance jigon jam'iyyar PDP a ranar 26 ga watan Disamba, 1967.
10) Philip Shaibu
An haifi Shaibu, mai takarar gwamna a jihar Edo a ranar 1 ga watan Disamba, 1969.
A yanzu haka, Shaibu ne mataimakin gwamnan jihar.
Obi ya jinjinawa Atiku a shekaru 77
A wani labarin, mun ji cewa dan takarar jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya don taya Atiku Abubakar murna, yayin da ya cika shekaru 77 a duniya.
Obi a wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) ya jinjinawa dan takarar na jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku wanda ya bayyana a matsayin babban yayansa kuma jagora.
Asali: Legit.ng