CBN Zai Rufe Asusun Bankunan Jama'a Kan Dalili 1 Tak Zuwa Farkon 2024, Ya Fadi Dalili

CBN Zai Rufe Asusun Bankunan Jama'a Kan Dalili 1 Tak Zuwa Farkon 2024, Ya Fadi Dalili

  • Babban Bankin CBN ya fitar da sabuwar sanarwa kan rufe asusun bankunan jama'a daga watan Afrilu na sabuwar shekara da za mu shiga
  • CBN ya sanar da cewa dukkan asusun bankunan da ba su da lambobin BVN da NIN za su fuskanci barazanar rufe wa
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a yau Juma'a 1 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya, CBN ya sanar da kulle asusun bankunan jama'a da ba su da lambobin BVN da NIN.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a yau Juma'a 1 ga watan Disamba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke mummunan hukunci kan Sarkin Fulani da wasu mutum 2 kan zargin garkuwa da mutane

CBN zai rufe asusun bakuna a farkon shekarar 2024 masu matsaloli
CBN Zai Rufe Asusun Bankunan a Najeriya da Su Ke da Tarun Matsaloli. Hoto: CBN.
Asali: UGC

Wane sanarwa CBN ya yi?

CBN ya ce dukkan asusun bankunan da su ke da matsala za a rufe su ne daga watan Afrilu na shekarar 2024, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin har ila yau, ya tura wannan sabon umarni ga dukkan rassan bankunan kasuwanci da ke fadin kasar baki daya.

Matakin rufe asusun bankunan zai zama an hana kudaden cikin asusun fita har sai lokacin da wa'adin matakin zai kare.

Mene dalilin daukar matakin na CBN?

Bankin ya ce wannan mataki zai inganta harkokin kudade da kuma samar da tsaro a asusun bankunan jama'a.

Ya kuma ce za a tabbatar an yi amfani da lambobin BVN da kuma NIN yayin bude sabon asusun banki, cewar The Nation.

Daga watan Janairun 2024 za a sabunta dukkan asusun bankuna inda za a hada dukkan asusun bakunan da lambobin BVN da kuma NIN.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tashin hankali yayin da jami'an NSCDC suka harbi dalibai a Abuja yayin jarrabawa

Kotu ta yi hukunci kan amfani da sabbin kudade

A wani labarin, Bankin CBN ta ba da umarni kan ci gaba da amfani da sabbin takardun kudade.

Wannan na zuwa ne yayin da jama'a ke fargabar amfani da tsaffin kudaden yayin da wa'adinsu ya zo karshe.

A kwanakin baya ne Koli Koli ta yi hukunci kan amfani da tsaffin kudade tun bayan kirkirar sabbin kudaden da ake amfani da su a harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.