Kano: Shin Akwai Alamun Nasara Ga Gwamna Abba da Gwamnonin PDP 2 da Aka Rusa Zabensu? An Yi Bayani

Kano: Shin Akwai Alamun Nasara Ga Gwamna Abba da Gwamnonin PDP 2 da Aka Rusa Zabensu? An Yi Bayani

Kotun Daukaka Kara ta kwace kujerun akalla gwamnoni uku tun bayan fara sauraran kararrakin zabe bayan kammala zaben 2023.

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano da Dauda Lawal na jihar Zamfara da kuma Caleb Mutfwang na Plateau su ne ke cikin matsala a kwanakin nan.

An yi hasashen yadda za ta kaya a shari'ar zaben Kano, Plateau da Zamfara
Jihohin Kano da Plateau da Zamfara na dakon abin da zai kasance a Kotun Koli. Hoto: C. Mutfwang, A. Kabir, D. Lawal.
Asali: Twitter

Mene ya faru a Kano?

Kotun Daukaka Kara ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir da ke karkashin jam’iyyar NNPP kan zargin cewa ba dan jam’iyyar ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin kotun ya sha bamban da na kotun zabe wacce ita ma ta rusa zaben gwamnan a baya.

Jam’iyyar APC da dan takararta, Nasiru Gawuna su na kalubalantar zaben gwamnan da aka gudanar a watan Maris.

Kara karanta wannan

APC ta mamaye Majalisar jihar PDP bayan kotu ta kwace dukkan kujeru 16, an shiga yanayi

Matawalle da Lawal a Zamfara

A jihar Zamfara kuma, Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan zaben da ya bai wa Gwamna Dauda Lawal dare nasara a matsayin wanda bai kammala ba.

Kotun ta umarci hukumar zabe ta INEC da ta sake gudanar da zabe a kananan hukumomi guda uku saboda wasu matsaloli.

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle na kalubalantar zaben Dauda Lawal da aka gudanar a watan Maris.

APC da PDP a Plateau

Hukunci na uku shi ne rusa zaben Gwamna Caleb Mutfwanfg na jihar Plateau wanda ya fito takara a jam’iyyar PDP.

A ranar 17 ga watan Nuwamba kotun ta rusa zaben saboda jam’iyyar PDP ba ta da tsari da za ta iya daukar nauyin ‘yan takararta.

Dan takarar jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda Gushwe shi ke kalubalantar zaben Caleb da aka gudanar a watan Maris.

Shin akwai wani haske tare da gwamnonin?

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta bayyana ainahin wanda ya lashe zaben gwamnan Kebbi

Dukkan gwamnonin sun daukaka kara zuwa kotun gaba don kalubaantar hukuncin kotunan.

Lauya Lawal Lawal yayin hira da BBC, ya ce Gwamna Dauda Lawal ya fi kowa alamun nasara a cikin wadanda aka Koran.

Lauyan ya ce makomar Dauda ta ta’allaka ne ga jama’ar kananan hukumomin da za a sake zabe madadin kotu.

Sai dai wani mai fashin baki a siyasa, Olakawon Gaffar ya shaidawa Legit cewa ba za a iya yanke hukunci yanzu ba amma akwai hasken kotun koli za ta yi adalci.

Jerin gwamnonin da aka kwace kujerunsu

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta kawace kujerun wasu gwamnoni uku a Arewacin Najeriya.

Gwamnonin sun hada da Gwamna Abba Kabir na Kano da Caleb Mutfwang na Plateau da kuma Dauda Lawal na Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.