Da Gaske Gwamna Caleb Mutfwang Na Plateau Na Nuna Wariya Ga Musulmai? Gaskiya Ta Fito
- Yayin da ake yada cewa Gwamna Caleb na jihar Plateau na nuna wariya ga Musulmai, kungiyar Musulmi ta karyata hakan
- Al'ummar Musulmai a jihar sun bayyana irin gudunmawa da kuma mukamai da gwamnan ya bai wa Musulmai
- Kakakin kungiyar, Mubarak Isa shi ya bayyana haka inda ya ce gwamnan ya na da kyakkyawan alaka da su
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Al'ummar Musulmi a jihar Plateau sun karyata jita-jitar cewa Gwamna Cale Muftwang na jihar Plateau na nuna musu wariya.
Musulman su ka ce Gwamna Caleb na iya bakin kokarinsa wurin tabbatar da adalci a tsakninsu da Kiristoci.
Mene kungiyar ke cewa kan Caleb na Plateau?
Kungiyar ta bayyana haka a yau Alhamis 30 ga watan Nuwamba yayin ganawa da manema labarai a Jos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin kungiyar, Mubarak Isa shi ya bayyana haka inda ya ce gwamnan ya na da kyakkyawan alaka da su.
Isa ya ce dalilin haka nema ya saka gwamnan nada Musulmai manyan mukamai a jihar a cikin watanni shida kacal da ya yi, cewar Tribune.
Ya ce duk masu yada jita-jitar nuna wariyar kawai su na yi ne don bata alakar da ke tsakaninsu.
Wasu mukamai Caleb na Plateau ya nada?
Ya ce:
"Mun zo nan ne don nuna goyon baya ga Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau da irin ci gaban da ya kawo a watanni shida.
'Mu na son yin amfani da wannan dama don tabbatar da cewa Mutfwang ya kasance mai son zaman lafiya da hadin kai.
"Wannan na daga cikin dalilan da ya sa mu ke son nuna wa duniya irin ci gaba da kuma mukamai da ya bai wa Musumai."
Mubarak ya kara da cewa Muftwang ya nada Hamisu Anani a matsayin shugaban karamar hukumar Wase, cewar The Sun.
Har ila yau, ya ce Muftwang ya nada Danladi Kwari a matsayin shugaban hukumar Alhazai a jihar, sai Dayyabu Dauda sakataren hukumar.
Sauran sun hada da kwamishinoni kamar Bashir Lawandi da Muhammed Inuwa da Hajiya Jamila Tukur.
Lalong na shirin yin murabus
A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong na shirin yin murabus daga mukamin Minista.
Wannan na zuwa ne bayan Lalong ya samu nasara a kotu da a ba shi kujerar Sanata.
Asali: Legit.ng