Kotu Ta Dauki Mataki Kan Matar da Ta Lakadawa Mijinta Duka Saboda Yana Hira da Yan Mata

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Matar da Ta Lakadawa Mijinta Duka Saboda Yana Hira da Yan Mata

  • Wata mata da ta lakadawa mijinta dukan kawo wuka a Kano ta fuskanci hukuncin kotun majistire da ke Rijiyar Lemu
  • An gurfanar da matar ne mai suna Hafsa bisa zarginta da yi wa mijinta dukan tsiya kan zargin yana hira da 'yan mata a waya
  • Mai shari'a Umar Sanusi Dan Baba ya bayar da ajiyar Hafsa a gidan gyaran hali har zuwa ranar 11 ga watan Disamba, 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Kotun majistire da ke Rijiyar Lemu, jihar Kano, ta bayar da ajiyar wata mata, Hafsa Ibrahim a gidan gyara hali kan lakadawa mijinta Jamilu Muhammad duka.

Matar ta lakadawa mijinta duka ne da wayar dutsen guga, tare da kekketa masa suturarsa har kala casa'in kan zargin yana hira da 'yan mata a wayarsa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar mai taimakon Boko Haram da kudade da kuma DSS, ta fadi dalili

Kotun majistire/Miji da mata
Kotu ta garkame matar da ta lakadawa mijinta dukan tsiya kan ta kama shi yana hira da 'yan mata a waya Hoto: Nigeria Police
Asali: Twitter

Hafsa ta karyata zargin ta duki mijinta Jamilu

Mai shigar da kara, Usman Shuaibu Dala, ya shaida wa kotun cewa Hafsa ta ji wa mijinta rauni bayan dukansa a kai da dutsen guga, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk da haka matar ba ta hakura ba, sai da ta sanya almakashi ta yanka kala casa'in na suturar mijin tare da kwace masa wayarsa da ta kai naira dubu tamanin."

A cewar mai gabatar da karar.

Sai dai, Hafsat ta karyata wannan zargi da ake yi mata.

Mai shari'a Umar Sunusi Dan Baba, ya dage sauraron karar zuwa 11 ga watan Disamba, 2023.

Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa kan kashe jami'an DSS 7

A wani labarin, wata babbar kotu da ke Ikeja ta samu wasu mutane biyu da laifin kisan wasu jami’ai bakwai na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

Alkalin kotun, Hakeem Oshodi, ya yankewa Clement Ododomu hukuncin kisa ta hanyar rataya da Tiwei Monday daurin shekaru 16 a gidan yari.

Laifukan da ake tuhumar wadanda ake zargin sun aikata

Rahoton The Cable ya bayyana cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 14 ga Satumba, 2015, a Ishawo Creek, Ikorodu, Legas.

An gurfanar da su ne a kan tuhume-tuhume 10 da ke da alaka da hada baki wajen aikata kisa da kisa da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da ya ci karo da sashe na 223 da 298 (3) na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel