Murna Yayin da a Karshe FG Ta Bayyana Ranar Biyan Basukan Masu Cin Gajiyar N-power, Ta Fadi Dalilai
- Matasa masu cin gajiyar N-Power za su more kwanan nan bayan sanarwar Ministar jin kai da walwalar jama’a, Betta Edu
- Dakta Edu a bayyana cewa a watan Nuwamba da Disamba za su yi gyare-gyare yayin da biyan kudaden zai fara a watan Janairun 2024
- Legit Hausa ta ji ta bakin mataimakin shugaban kungiyar matasan N-Power a Gombe, da sakataren kungiyar ta kasa
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Ministar Jin Kai da Walwala, Dakta Betta Edu ta bayyana ranar biyar basukan masu cin gajiyar N-Power.
Betta Edu ta ce su na saran fara biyan ne a watan Janairun shekarar 2024 ganin yadda su ke ci gaba bincike, Legit ta tattaro.
Mene Edu ta ce kan biyan basukan N-Power?
Edu ta bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a gidan talabijin na News Central da Legit ta leko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministar ta ce gwamnatin Tinubu ta himmatu wurin tabbatar da tsari mai kyau a shirin na N-Power.
Ta ba da tabbaci ga masu bin basuka har da wadanda su ka kammala wa’adinsu za su samu kudadensu.
Ta ce:
“Mun samu matsaloli a shirin, kuma muna son gyara komai da ke ciki da kuma biyan basuka da kawo gyara a cikin shirin.
“Za mu dauki bayanai na mutane mu saka su a cikin shirin da kuma tantance su, sannan mu biya su kudadensu.”
Edu ta ce Bola Tinubu ya ba su umarnin biyan dukkan tarun basukan matasan da ke cin gajiyar N-Power.
Ta kara da cewa:
“Bangaren N-Power, mu na rokon ‘yan Najeriya da matasa su bamu zuwa nan da watan Janairun 2024.
“Saboda akwai matsaloli a cikin shirin wanda za mu yi gyara a watan Nuwamba da Disamba, sannan biyan kudade a watan Janairu.”
Har ila yau, Sakataren kungiyar matasan ta kasa, Bashir Kadan ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan yaudara ta Gwamnatin Tarayya.
Ya ce:
"Gaskiya ba mu ji dadi ba, da farko mun je Abuja mun yi ganawa da shugaban shirin N-Power, Dakta Akindele inda ya yi alkawarin cewa a watan Nuwamba za a biya.
"Mun sanar da mabiyan mu cewa za a biya, amma har yau 29 ga watan Nuwamba ba a biya ba.
A karshe, ya ce a matsayinsu na kungiya sun yi Allah wadai inda ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggawar biyansu hakkokinsu.
Mataimakin shugaban kungiyar masu cin gajiyar N-Power a Gombe, Adamu Muhammad Haram ya ce wannan yaudara ce kamar ta kullum.
Ya ce:
"Duk wanda ya ke cin gajiyar N-Power ba zai yi maraba da wannan batu ba don an sha yi mana alkawari.
"Allah ne kawai ya san iyakar wannan kullum ace za a biya ranar kaza sai ace wai ana bincike, haka aka shafe watanni tara."
FG ta magantu kan biyan basukan N-Power
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan basukan da masu cin gajiyar N-Power ke bi.
Wadanda ke bin bashin mafi yawanci 'yan rukunin 'C' ne da aka dauka a shekarar 2021 inda wasu ke bin bashi har na tsawon watanni tara.
Asali: Legit.ng