JAMB Ta Bayyana Ranar da Za a Fara Rijistar Jarrabawar UTME Na 2024, Ta Ba Da Shawara

JAMB Ta Bayyana Ranar da Za a Fara Rijistar Jarrabawar UTME Na 2024, Ta Ba Da Shawara

  • Hukumar JAMB ta sanar da ranar fara jarrabawar UTME na sabuwar shekarar 2024
  • JAMB ta ce za a fara siyar da fom na jarabawar a ranar 15 ga watan Janariu zuwa 26 ga watan Faburairu
  • Ta ce jarabawar kuma za a gudanar ta ita ne daga ranakun 19 ga watan Afrilu zuwa 29

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar Jarabawa ta JAMB ta fitar da sanarwar ranar da za a gudanar da jarabawar UTME ta shekarar 2024.

Hukumar ta ce za ta fara siyar da fom na jarabawar a ranar 15 ga watan Janairu zuwa ranar 26 ga watan Faburairu.

Hukumar JAMB ta fitar da sanarwa kan shirin jarabawar shekarar 2024
JAMB ta fitar da sanarwa kan shirin jarabawar 2024. Hoto: JAMB.
Asali: Twitter

Wane sanarwa hukumar JAMB ta fitar?

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin jami'in yada labarai Fabian Benjamin, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benjamin ya ce jarabawar za a gudanar da ita ne a ranar 19 zuwa 29 ga watan Afrilu na shekarar 2024.

Ya ce jarabawar gwaji kuma ta 'Mock' za a gudanar da ita ne a ranar 7 ga watan Maris na shekarar 2024, cewar The Guardian.

Shawarar hukumar JAMB ga dalibai

Sanarwar ta ce:

"Kamar yadda aka tattauna har na tsawon kwanaki biyu, JAMB ta fitar da sanarwa kan shirye-shiryen gudanar da jarabawar UTME.
"JAMB ta saka ranar 15 ga watan Janairu zuwa 26 ga watan Faburairun shekarar 2024 don siyar da fom na rijista.
"Mu na shawartar masu zana jarabawar da su fitar da takardar jarabawarsu zuwa 10 ga watan Afrilu inda za a fara jarabawar daga 19 zuwa 29 ga watan Afrilun 2024."

Kara karanta wannan

Alkalluma: Yan Najeriya miliyan 1.8 na dauke da cutar kanjamau, Majalisar Tarayya ta dauki mataki

Benjamin ya shawarci masu zana jarabawar da su kula da lokacin zana jarabawar don kaucewa mantuwa.

Ya kuma shawarci daliban da su ziyarci shafin hukumar ta JAMB @www.jamb.gov don neman karin bayani.

An kama ma'aikacin hukumar JAMB da satar kwamfuta

A wani labarin, jami'an tsaro sun cafke wani ma'aikacin Hukumar JAMB kan zargin satar kwamfuta a ofishinta.

Wanda ake zargin ya na shara ne a hukumar inda ya bayyana cewa ya saci kwamfutar ce don ya biya kudin hayar gidansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.