Yan Fansho Ga Tinubu: Cire Tallafin Mai Ya Jefa Mu Cikin Mawuyacin Hali
- Yan fansho a Najeriya sun koka wa shugaban kasa Bola Tinubu kan halin da suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur
- Kungiyar 'yan fansho ta kasa (NUP) ta ce sun gabatar da bukata ga ministar jin kai don saka 'yan fansho a wani tallafin gwamnati
- Ba iya 'yan fansho ba, NUP ta ce cire tallafin mai ya jefa da yawan talakawa cikin halin kaka ni kayi, tare da rokon gwamnati ta yi abin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Akure, jihar Ondo - Kungiyar 'yan fansho ta kasa (NUP) ta koka kan janye tallafin man fetur, tana mai cewa hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali, duk 'yan fansho na ji a jikinsu.
Shugaban kungiyar Mista Godwin Abumisi ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen taron shugabannin kungiyar na kasa da aka gudanar a Akure.
Ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta cika alkawarinta na sanya 'yan fansho a shirin tallafawa talaka da naira dubu 25 don rage radadin cire tallafin man.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me kungiyar NUP ke nema daga gwamnatin Tinubu?
Jaridar Vanguard ta ruwaito jawabin shugaban NUP, inda yake cewa:
"An gudanar da bikin ranar 'yan fansho ta wannan shekarar a ranar 5 ga watan Oktoba, kuma gwamnatin tarayya ce ta ware wa 'yan fansho wannan rana.
"Mun samu ganawa da ministar jin kai, Dr Betta Edu kuma muna fatan za a sanya mu a shirin bayar da tallafin naira dubu 25 na gwamnatin tarayya."
Abumisi ya ce ko ba su fada ba za a gane cire tallafin mai ya jefa 'yan fansho cikin tsaka mai wuya, ga yawan damuwa, hatta ga talakawan kasar baki daya, rahoton Tribune Online.
"Da wannan muke rokon gwamnatin tarayya da ta jihohi su taimaka su yi abinda ya dace cikin gaggawa don rage radadin azabar da talakawa ke sha a wannan lokaci."
A cewar Abumisi.
Yan fansho za su fara azumi a Legas
A wani labarin daban, kun karanta cewa a kokarin 'yan fansho na cimma bukatunsu na ganin an gyara duk wasu kura-kurai a tsarin fansho na 'CPS', masu karbar fansho a jihar Lagas za su fara azumi da addu'o'i a ranar Alhamis.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Shugaban kungiyar yan fansho na kasa reshen jihar Lagas, Michael Omisande, ne ya bayyana hakan a cikin sakon da ya saki, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng