Yan Fansho Sun Aike da Wata Muhimmiyar Wasika Ga Shugaba Buhari

Yan Fansho Sun Aike da Wata Muhimmiyar Wasika Ga Shugaba Buhari

  • Yan fansho sun nuna matukar jin daɗinsu ga shugaba Buhari a wata wasika da suka rubuta masa
  • Yan fanshon ƙarkashin kungiyarsu ta kasa sun rubuta wasikar godiya da jinjina ga shugaban
  • Wannan dai ya biyo bayan umarnin da Buhari ya bayar na biyan yan fansho bashin da suke bi na shekara biyu

Abuja:- Ƙungiyar yan fansho ta ƙasa ta rubutawa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wasika ta musamman domin jinjina masa, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

Wasikar yan fanshon dai godiya ce da fatan alkairi biyo bayan biyansu wasu kuɗaɗe da suke bin gwamnatin tarayya bashi da shugaban yayi.

Takardar wasikar wacce take ɗauke da sanya hannun shugaban yan fansho na kasa, Elder Actor Zal, da kuma sakatarensa, sun jinjina wa shugaba Buhari bisa wanna namijin kokari.

Shugaba Buhari
Yan Fansho Sun Aike da Wata Muhimmiyar Wasika Ga Shugaba Buhari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yan fanshon sun bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba dake sauraron matsalolin al'umarsa kuma wannan matakin yasa yan fansho cikin annashuwa.

Kara karanta wannan

Babu Yaren da FG Take Fahimta Sosai Kamar Yajin Aiki, Kungiyar Likitoci Ta Yi Karin Haske

Me wasikar yan fansho ta kunsa?

A cikin takardar da kungiyar yan fanshon ta rubuta zuwa ga shugaba Buhari, sun ce:

"A madadin shugabannin wannan kungiya da mabobinta baki daya muna mika sakon godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari, kan ba da umarnin biyanmu hakkokin mu na shekaru biyu."
"Duk da halin matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, an ba da umarnin biyanmu na watanni 12, sai kuma wasu watanni 6 a watan Yuni, da kuma karin wasu watanni 6 da muke sa ran karba a kowanne lokaci."

Shin gwamnati ta gama biyansu kenan?

Yan fanshon sun kara da cewa muna fatan nan gaba kaɗan mu samu ragowar hakkokinmu na tsawon watanni shida da ya rage.

Daga karshe yan fanshon sun kara jinjina ga shugaba Buhari, inda suka ce: "Bamu da kalmar da zamu gode maka da ita."

Wane irin matsin tattalin arziki Najeriya ke ciki

A wani labarin kuma Gwamnonin ƙasar nan sun bayyana cewa suna iyakar bakin kokarinsu duk da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Jam'iyyar APC Ta Cire Kakakin Majalisar Dokoki Daga Wani Mukami

Shugaban kungiyar gwamnonin ƙasar nan kuma gwamnan jihar Ekiti , Kayode Fayemi, yace gwamnoni suna iyakar kokarin da zasu iya duk da karancin kuɗaɗen shiga.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin jawabi a wurin kaddamar da hanya mai kilomita 4.3Km a Minna, babban birnin jihar Neja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262