Shugaba Tinubu Ya Bayar da Muhimmin Umarni Kan Iyakokin Najeriya, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a tabbatar da tsaron iyakokin ƙasar nan
- Ministan harkokin cikin gida Tunji-Ojo shi ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels tv
- Ministan ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya buƙaci ma'aikatar ta samar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin rashin tsaro a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ma’aikatar harkokin cikin gida umarnin tabbatar da tsaron iyakokin Najeriya, a cewar ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo.
Tunji-Ojo ya bayyana haka ne a yammacin ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na 'Politics Today'.
Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya buƙaci ma’aikatar da ta samar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin rashin tsaro a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane umarni Shugaba Tinubu ya bayar?
Ministan ya ce:
Ƙasa na samun kwanciyar hankali ne idan kan iyakarta da tsaro. Ya kamata mu fahimci hakan yanzu, sannan ba gudu ba ja da baya kan hakan."
"Shugaban ƙasa ya nace a kan hakan, ya ba mu umarni a matsayin mu na ma'aikatar cikin gida mu tsare waɗannan iyakokin."
"Sannan tabbas sai an haɗa da kayayyakin fasaha, saboda yanzu ba 2003 bane, yanzu muna 2023 ne."
"Saboda haka rawar da fasaja ke taka wa wajen samar da mafita wurin gudanar da ayyuka na da matuƙar muhimmanci."
Ya cigaba da cewa:
"Mun yi duba kan batun gudunmawar da jama'a za su bayar wanda ya ke da matuƙar muhimmanci, saboda za ka iya kare mutane ne kawai idan suna son a kare su. Wannan shi ne gaskiya. Mun ga abin da ya faru a Afghanistan, mun ga abin da ya faru a Iraq, abin da ya faru a Libya."
"Idan jama'a ba su ba ka goyon baya ba, ba su ba ka gudunmawar da ka ke buƙata ba, zai zama da wahala ka iya magance matsalar rashin tsaro."
"Hakanan ana buƙatar fasaha. Amma ba zan so in gaya muku fasahar da muke duba a kai ba."
Tinubu Zai Sake Ciyo Bashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa kan sake karbo bashin dala biliyan 8.69.
Shugaba Tinubu a cikin tsarin karbar bashin Gwamnatin Tarayya daga shekarar 2022 zuwa 2024 zai karɓi Yuro miliyan 100.
Asali: Legit.ng