Dakarun Sojoji Sun Sama Nasara Kan Yan Ta'adda a Taraba, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

Dakarun Sojoji Sun Sama Nasara Kan Yan Ta'adda a Taraba, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu galaba kan miyagun ƴan masu yin garkuwa da mutane a birnin Jalingo na jihar Taraba
  • Dakarun sojojin sun kai sumame ne kan maɓoyar ƴan ta'addan inda suka fatattake su tare da ceto mutum biyu da suka yi garkuwa da su
  • Da yawa daga cikin masu garkuwa da mutanen sun arce bayan ganin jami'an tsaro amma an samu nasarar cafke biyu daga cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a wata unguwa da ke bayan garin birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Sojojin sun ceto mutanen da aka sace ɗin ne a kewayen CBN-Babayau a ƙaramar hukumar Jalingo, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun fatattaki yan bindiga a jihar Arewa, sun ceto mutanen da suka sace

Sojoji sun fatattaki masu garkuwa da mutane a Taraba
Dakarun sojoji sun ceto mutum biyu da aka sace a Jalingo Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da kwamandan runduna ta 6 ta sojojin Najeriya, Birgediya Janar Frank Etim ya fitar, rahoton Premium Times ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka samu galaba kan ƴan ta'addan

A cewarsa, an samu nasarar hakan ne a safiyar ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba, 2023, a lokacin da sojoji bisa sahihan bayanan da suka samu suka kai sumame a maɓoyar ƴan ta'addan.

A cewarsa ƴan ta'addan suna da maɓoya a babban birnin jihar, inda su ke kitsa ayyukansu.

A yayin farmakin, an cafke mutum biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen, yayin da wasu suka gudu bayan ganin dakarun sojojin.

"Sojojin sun bi bayansu kuma nan ba da daɗewa ba za su cafke su." A cewar kwamandan.

A halin da ake ciki, ya yaba da ɗaukin da sojojin suka kai a kan lokaci, ya kuma umurce su da kada su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron al'umma.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin rundunar sojojin sama sun halaka kasurgumin shugaban yan ta'addan Boko Haram

Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan sakai sun fatattaki ƴan binɗiga a ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutum shida da miyagun ƴan bindigan suka sace sumamen da suka kai maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng