Dalilai 3 da su ka sa aka dakatar da Jami'ar Datti Baba-Ahmed shiga makarantar lauyoyi na shekaru 5

Dalilai 3 da su ka sa aka dakatar da Jami'ar Datti Baba-Ahmed shiga makarantar lauyoyi na shekaru 5

Cibiyar kula da Bangaren Shari’a (CLE) ta sanya takunkumi na shekaru biyar a tsangayar shari’a da ke Jami’ar Baze da ke birnin Tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Cibiyar CLE ta sanya dokar ce bayan zargin wuce gona da iri wurin bayar da gurbin karatu a tsangayar karatun lauya na fiye da mutane 50 a shekara.

Manyan dalilan dakatar da Jami'ar Datti Baba-Ahmed na shia makarantar lauyoyi
An dakatar da Jami'ar har na tsawon shekaru biyar. Hoto: @bazeuni_abuja.
Asali: Twitter

Cibiyar ta bayyanna haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren rikon kwarya na hukumar, Aderonke Osho ta fitar yayin hira da Channels TV.

Legit ta tattaro dalilan da su ka jawo sanya dokar a Jami’ar Baze:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kaciyar mata: Gwamnan PDP ya haramta al'adar a fadin jiharsa, an bayyana illarta ga mata

1. Saba dokar adadin gurbin karatu

Kamar yadda cibiyar ta sanar, Jami’ar ta saba dokar bayar da gurbin karatu a tsangayar lauyoyi har mutane 50 a shekara.

A dalilin haka, a yanzu tsangayar ta na da dalibai fiye da 347 da ke jiran shiga makarantar lauyoyi ta Najeriya.

2. Bayar da gurbin karatu ga dalibai 750 a shekaru bakwai

CLE ta kara da cewa Jami’ar ta bayar da gurbin karatu ga dalibai 750 tun a shekarar 2017 wanda hakan ya saba ka'adar hukumar.

Cibiyar ta ce ya kamata shakarun su kai 15 don samun damar daukar wadannan dalibai a Jami’ar kamar yadda cibiyar ta tsara.

3. Kammala karatun lauya cikin shekaru uku

Har ila yau, an samu Jami’ar Baze da laifin kammala karatun lauya a shekaru uku kacal a ba tare da samun amincewar hukunar NUC ko CLE ba.

A ka’idar hukumar NUC, karatun lauya a Jami’a dole ya kai akalla shekaru 5 ko kuma shekaru hudu ga wadanda su ka fara a aji biyu.

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

Har ila yau, CLE ta bayyana cewa idan ba a samu sauyi ba, za ta iya kara wa'adin dokar fiye da shekaru biyar.

Na kusa rasa aiki saboda Jami'ar Baze, Bala Mohammed

A wani labarin, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana yadda ya kusa rasa aikinsa saboda bai wa Jami'ar Baze fili a Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya kusa raba shi da kujerar Ministan Abuja a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.