Makarantar Lauyoyi Ta Najeriya Za Ta Hukunta Dalibi Saboda Ya 'Kafa Baki Ya Sha Ruwan Gora' A Wurin Cin Abinci

Makarantar Lauyoyi Ta Najeriya Za Ta Hukunta Dalibi Saboda Ya 'Kafa Baki Ya Sha Ruwan Gora' A Wurin Cin Abinci

  • Makarantar Horas Da Lauyoyi Ta Najeriya da ke Legas ta tura wa wani dalibinta wasikar neman ba'asin dalilin da yasa ya kafa baki ya sha ruwa daga gora a wurin cin abinci duk da akwai kofi a tebur a gabansa
  • Wasikar da mahukuntar makarantar lauyoyin suka tura da ya bazu a intanet ya ce abin da dalibin ya aikata ya saba wa saba doka ta 6 (29) na kudin tarbiyya na daliban makarantun lauyoyi na Najeriya kan tarbiyar cin abinci da halayya
  • Makarantar ta bukaci dalibin ya amsa wasikar cikin awanni 24 da samunta ya bayyana dalilin da yasa ba za a hukunta shi ba saboda saba dokar

Jihar Legas - Makarantar Horas da Lauyoyi Ta Najeriya da ke Jihar Legas, a halin yanzu tana bincike kan wani dalibi da ya sha ruwa daga gora a wurin liyafar cin abinci.

Kara karanta wannan

Buhari: Tausayin Talaka ya sa na ki biyewa masu bada shawarar janye tallafin man fetur

Binciken zai iya sanadin mahukunta makarantar su dakatar da dalibin, SaharaReporters ta ruwaito.

Wasika Daga Makarantar Horas Da Lauyoyi.
Makarantar Lauyoyi Ta Najeriya Za Ta Hukunta Dalibi 'Ya Kafa Baki Ya Sha Ruwan Gora' A Wurin Cin Abinci. @SaharaReporters.
Asali: Twitter

Wani takardar neman jin ba'asi da mahukunta makarantar suka aike wa daliban, da ya bazu a intanet, ya ce dalibin ya saba doka ta 6 (29) na kudin tarbiyya na daliban makarantun lauyoyi na Najeriya kan tarbiyar cin abinci da halayya.

"An kai wa Direktan kuma shugaban sashin karatu a ranar 16 ga watan Yunin 2022 cewa yayin liyafar cin abinci na dalibai masu karatun lauyoyi a dakin cin abinci, an gano ka kafa bakinka a robar ruwa a yayin da kofin gilashi na kan teburinka," a cewar wasikar da wani Fagbemi Charles-Titilayo ya rattaba wa hannu a madadin Direkta kuma Shugaban Sashin Karatu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Don haka, ana bukatar ka yi bayanin dalilin da yasa ba za a hukunta ka ba saboda saba wa doka ta 6 (29) ) na kudin tarbiyya na daliban makarantun lauyoyi na Najeriya kan tarbiyar cin abinci da halayya.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Najeriya ya samu sauki bayan ya kwanta jinya a asibitin kasar waje

"Ka tura dalilanka, idan akwai zuwa ga Direkta kuma Shugaban Sashin Karatu cikin awa 24 da samun wannan wasikar."

Wata lauya ta yi tsokaci kan lamarin

Wakilin Legit Hausa ya tuntubi wata lauya mazauniyar Jihar Kaduna wacce ta nemi a sakaya sunanta don samun karin bayani game da lamarin, a hirar da aka yi da ita ta wayar tarho.

Ka kada baki ta ce tabbas abin da dalibin ya yi ya saba doka ta kuma irin tarbiyya da ake bawa lauyoyi a yayin da suke makarantar horaswar.

"Eh, hakan bai nuna kamun kai da kamala ba kuma shi lauya kowane lokaci kamata ya yi ya rika nuna halayen kamala da kamun kai.
"Dama dalilin liyar cin abincin (dinner) shine don koyar da irin wadannan tarbiyyar yayin cin abinci a teburi.
"An ajiye masa kofi, mai yasa bai yi amfani da shi ba? Kuma ana koyar da dalibai kafin cin abincin."

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Kasa: Jagoran Sasanci Da 'Yan Bindiga Ya Janye, Ya Sanar Da Mawuyacin Halin Da Fasinjojin Ke Ciki

Da aka mata tambaya ko wannan dokar na aiki kan lauyoyi bayan sun kammala karatunsu a makarantar horaswar sun fara aiki, ta ce:

"Eh, ba kan daliban makarantar horas da aikin lauya dokar ta tsaya ba.
"Ana iya hukunta kowanne lauya kan hakan (amma hakan bai cika faruwa ba) daga mutum ya kammala makarantar lauya, ba a cika damuwa sosai da wadannan abubuwan ba."

An Rage Wa Wasu Farfesoshi Uku Mukami a Jami'ar Adamawa

A wani rahoton, Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da karatu, Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, Farfesa Muhammad Ja'afaru, ne ya sanar da hakan a bikin cika shekara uku na Farfesa Abdullahi Tukur, Shugaban MAU, a ranar Asabar a Yola.

Ya ce an mika batun ga sashin hukunta masu laifi a jami'ar kuma aka amince da rage wa malaman da abin ya shafa mukami.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel