Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

- Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi ya bada labarin yadda ya kusa rasa aikinsa a lokacin yana ministan Abuja

- Gwamna Mohammed ya ce hakan ya faru ne sakamakon filin da ya bawa Jami'ar Baze ta Abuja

- A cewar gwamnan akwai wata mata da ke son filin amma ya dage wurin ganin cewa jami'ar aka bawa filin

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana yadda ya kusa rasa aikinsa a matsayin ministan birnin tarayya Abuja, FCT, saboda bawa Jami'ar Baze fili a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke magana a ranar Alhamis yayin da wanda ya kafa jami'ar, Yusuf Ahmed da ma'aikatansa suka kai masa ziyarar ban girma a Bauchi, gwamnan wanda ya yi aiki a matsayin minista a karkashin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ya ce wata mata da ba san ko wacece bace tana son filin da ya bawa jami'ar.

Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze
Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Ya ce ya bar wa kansa wannan batun na tsawon lokaci amma a yanzu yana ganin lokaci ya yi da zai bayyana.

DUBA WANNAN: Alkali ya yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda haike wa wata a Jigawa

"Ku san alaka ta da Baze sosai, gwagwarmayar da muka yi. Wata mata ta so kwace filin ka. Na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze, amma akwai abinda ba ku sani ba kuma yau na fada.

"Ba abinda ba zan iya yi ba domin samar da abinda zai amfani al'umma kuma abin da na yi maka kenan. Na yi imanin shine abinda ya dace.

"Na yi hakan ne saboda bana son fili ya shiga hannun wadanda za su yi abu mara alheri da shi ne. Na taya ka murna kuma ina alfaharin yin hulda da kai," in ji Mohammed.

Gwamnan ya ce yana farin ciki a duk lokacin da na ga ana tallata jami'ar a gidajen talabijin na duniya.

KU KARANTA: 'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu

Gwamna Mohammed ya ce yana maraba da tayin da jami'ar ta yi wa jiharsa na ragin kudin makaranta na 75% ga yan asalin jihar.

Wanda ya kafa jami'ar ya ce yana farin cikin yadda jami'ar ta bunkasa da taimakon Allah da kuma taimakon shugabanni irin su Gwamna Mohammed.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel