Gwamnan Kaduna Ya Fadi Gwaggwabar Kyauta Ga Wadanda Su Ka Lashe Musabaka, Bala Lau Ya Yi Martani
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya shawarci mutane da su rike Alkur’ani hannu bibbiyu don samun zaman lafiya a kasar
- Uba Sani ya bayyana gagarumar kyutar da zai yi wa duk wadanda su ka lashe gasar masabakar Alkur’an bangaren mata da maza
- A martaninshi, shugaban kungiyar Izakah, Sheikh Bala Lau ya ce duk wanda ya fahimci Alkur’ani ba zai taba yin ta’addanci ba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana gagarumar kyauta ga wadanda su ka ci nasarar lashe gasar musabaka a jihar.
Gwamnan ya ce wadanda su ka ci nasarar lashe gasar na daya da na biyu za su samu damar kasancewa cikin malaman da za su fadakar yayin aikin hajji.
Wacce kyauta Uba Sani ya yi alkawari?
Uba Sani ya ce kyautar ta shafi dukkan bangarorin mata da maza inda hakan zai kara musu kwarin gwiwar ci gaba da kokari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani ya bayyana haka ne yayin rufe gasar musabakar a yau Asabar 25 ga watan Nuwamba a Kaduna, Tribune ta tattaro.
Dadi da kari, gwamnan ya ware kyaututtukan kudade ga wadanda su ka yi nasara daga na daya zuwa na hudu a ko wane bangare.
Wane martani Bala Lau ya yi?
Yayin da ya ke bayyana muhimmancin Alkur’ani, gwamnan ya ce al’umma za su zauna lafiya idan har su na karanta Alkur’ani da kuma aiki da shi.
Yayin da ya ke jawabi, shugaban kungiyar Izalah Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce Alkur’ani shi ne maganin matsaloli har da ta’addanci a kasar.
Bala Lau ya ce idan har mutum ya fahimci Alkur’ani to ba zai taba shiga harkar ta’addanci ba da kuma fashin daji.
Ya kirayi malamai da su himmatu wurin koya wa mutane Alkur’ani don samun zaman lafiya a kasar.
Gwamna Uba Sani ya yi nasara a kotu
A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sanin a jihar Kaduna.
Kotun har ila yau, ta yi watsi da karar dan takarar PDP, Isa Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng