Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 11
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a wasu ƙauyuka guda uku na jihar Taraba
- A yayin harin da ƴan bindigan suka kai, rayukan mutum 11 da ba su ji ba, ba su gani ba sun salwanta
- Jama'ar yankin sun buƙaci hukumomi da su tura jami'an tsaro domin daƙile ayyukan ƴan bindigan ɗa suka addabe su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga a ranar Juma'a da yamma sun kai hari tare da kashe mutum 11 a ƙananan hukumomin Yantu da Ussa na jihar Taraba.
Ƴan bindigan, a cewar mazauna yankin, sun kai hari tare da kashe mutane tara a ƙauyukan Rubur Ribasi, Nyicwu da Ruwah ƙananan hukumomin da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
Mista Yakubu Tinya, wanda da ƙyar ya tsallake rijiya da baya, ya shaidawa Nigerian Tribune cewa maharan sun kuma kashe mutum daya a unguwar Tukwog, dake kan hanyar Takum-Manya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Sun zo da yawansu don korar jama'a da misalin ƙarfe 6:00 na yamma kuma suka kashe duk wanda suka gani. An kai wa wasu hari a gonakinsu, wasu a kan hanyarsu ta dawowa, wasu a gidajensu."
"Sun kai mana hari ni da ƴan uwana biyu, suka kashe ɗaya daga cikin mu. Wasu daga cikinsu Fulani ne, amma wasu kamar ba ƴan Najeriya ba ne."
Me hukumomi ke cewa kan harin?
A halin da ake ciki, Amb. Peter Shamwun, shugaban ƙaramar hukumar ta Ussa wanda ya tabbatar da harin a ranar Asabar, ya kuma ƙara da cewa ƴan bindigan sun kuma tare hanyar Takum-Ussa domin kashe ƙarin mutane.
A cewar shugaban ƙaramar hukumar, ƴan bindigar sun kuma kai hari a unguwar Kpambo Yashe da ke ƙaramar hukumar Ussa inda suka kashe mutum ɗaya.
Shugaban ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da Gwamna Agbu Kefas da su gaggauta tsara wata tawaga ta rundunar haɗin gwiwa ta JTF da ta ƙunshi sojoji da ƴan sanda da kuma ƴan sakai don fatattakar ƴan bindiga a yankin.
Sai dai, rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta bakin kakakinta, Usman Abdullahi ya ce ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 150
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki wasu garuruwa huɗu a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
A yayin htin da ƴan bindigan suka kai, sun yi awon da mutum 150 waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Asali: Legit.ng