Yadda Faston Da Ke Sayar da Tikitin Shiga Aljanna Ya Gusar da Hankulan Yayanmu, Ya Raba Mu

Yadda Faston Da Ke Sayar da Tikitin Shiga Aljanna Ya Gusar da Hankulan Yayanmu, Ya Raba Mu

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke malamin majami'a bisa laifin garkuwa da yara tara, da kuma laifin dirkawa matar ma'aikacinsa ciki
  • A shekarar 2022 ne aka gurfanar da faston gaban majami'a kan laifin damfarar naira dubu 310 kowanne da sunan zai basu tikitin shiga aljanna
  • A wannan karon, malamin majami'ar ya ce kama shi da aka yi a banza domin ya kammala wa'azin shekaru 42 da aka aiko shi yayi a duniyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ado-Ekiti, jihar Ekiti - Da alama dai Noah Abraham, shugaban majami'ar Christ High Commission da ke Omua-Oke, jihar Ekiti bai daddara ba.

Idan muka waiwaya baya lokacin da aka taso Abraham gaba kan damfarar wasu mabiyansa naira dubu dari 310 kowanne da sunan bayar da biza zuwa aljanna.

Kara karanta wannan

Miji ya zargi surukinsa hakimi, basarake a Kano da kashe masa aure tare da yunkurin tozarta shi

Fasto mai tikitin shiga aljanna
Duk da yana a hannun hukuma, Fasto Abraham ya ba zai damu da dauri ba domin ya kammala wa'azin da aka aiko shi ya yi a duniyar. Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Yanzu ma shugaban cocin ya sake bijiro da wata fatawa na cewa duniyar da muke ciki za ta shiga cikin rudani, da kuma alamto zuwan sabuwar duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Abraham ya sayar da tikitin shiga aljanna

A makon da ya gabata ne dai malamin majami'ar ya shiga hannun hukumar 'yan sandan jihar Ekiti, yanzu kuma ya ce bushararsa za ta girgiza duniyar nan, rahoton Vanguard.

Ana iya tuna cewa ranar 27 ga watan Afrelu, 2022 a Omuo-Ekiti, 'yan sanda suka cafke Abraham bayan karbar naira dubu 310 daga hannun sama da mutum 40 a wani sansani.

Malamin majami'ar ya karbi kudin ne da sunan zai ba mutanen tikitin shiga aljanna, lamarin da ya kaishi gaban kotin majistire, har dai aka ba da belinsa.

Na kammala wa'azina na shekaru 42 - Fasto Abraham

A ranar Alhamis din da ta gabata ne 'yan sandan jihar Ekiti tare da hadin guiwar hukumar hana safarar mutane (NAPTIP) suka kama malamin majami'ar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mene dalilin fadan sojoji da 'yan sanda da ya yi ajalin dan sanda? gaskiya ta bayyana

An kama malamin ne bisa zarginsa da hannu a sacewa tare da yin garkuwa da sama da mutane tara ciki har da kananan yara, da kuma laifin dirkawa matar ma'aikacinsa ciki.

Amma da ya ke zantawa da jaridar Vanguard, Fasto Abraham ya ce wannan kamawar an yi a banza, domin tuni ya kammala wa'azin da aka aiko shi ya yi a duniya.

Mata sun fito zanga-zanga tsirara a Anambra

A wani labarin, an rahoto mata na yin zanga-zanga tsirara a jihar Anambra kan kashe-kashe da ya addabi garin Awka.

Masu zanga-zangar sun karade babban birnin jihar dauke da kwalaye da ke nuni da batancin ransu kan cin hanci da rashawa da ya mamaye 'yan sandan jihar, rahoton Legit Hausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.