Wani Fasto mai siyar da tikitin shiga Aljannah ya shiga hannun hukuma
- Wani malami mai siyar da tikitin shiga Aljanna ya shia hannu
- Sai dai masu neman siyan tikitin sun yi zanga-zangar a sako shi
Hukumar yan sanda a kasar Zimbabwe ta kama wani Fasto tare da matarsa inda ake tuhumarsu da sayarwa da jama'a tikitin shiga aljanna.
Faston mai suna Tito ya bayyanawa dubban jama'a cewa Yesu Almasihu ne ya ba shi wannan tikiti domin ya sayar musamman ga wadanda suka kasance masu aikata zunubi domin su ma su samu damar shiga aljannar.
KU KARANTA: An kama wata babbar jigo a APC tana safarar mata zuwa turai
Ya ce "Ban damu da abinda mutane ko jami'an yan sanda ke cewa akai na ba, kawai nasan an kama ni ne saboda ina yin aikin ubangiji. Yesu Almasihu ne ya bayyana a gareni kuma ya bani tikiti tare da shaida min cewar na sayar da shi ga Jama'a domin su samu rabauta".
Yanzu haka dai dubban mutane ne ke yin zanga-zangar nuna adawa da kama Fasto din da aka yi, inda suke kira da hukumar yan sanda tayi gaggawar sakinsa, domin ko ma mai ya faru da kudinsu suke sayen tikitin ba da kudin wani ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng