Kungiyar Izala Ta Gayyaci Sheikh Idris Mukabala Kan Sakin Hannu da Yin Sallama Daya a Sallah

Kungiyar Izala Ta Gayyaci Sheikh Idris Mukabala Kan Sakin Hannu da Yin Sallama Daya a Sallah

  • Kwamitin wa'azi na ungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa'Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta aike da wasikar gayyatar mukabala ga Sheikh Idris
  • Ana sa ran mukabalar wacce aka shirya gudanar da ita ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba a Bauchi, za ta ilimantar da a'ummar Musulmi
  • Mukabalar za ta gudana ne tsakanin Sheikh Idris Abdul'azi, limamin masallacin Juma'a na Dutsen Tanshi, da Sheikh Dalhat Abubakar Kantana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bauchi - Kwamitin gudanar da wa'azin matasa na kasa reshen jihar Bauchi ya aike da wasikar gayyata ga Sheikh Idris Abdul'aziz don yin zaman mukabala da shi.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kwamitin matasan na jihar, Ustaz Ahmad Salihu Bukar, kwamitin ya ce za a gudanar da mukabalar don ilimantar da al'ummar Musulmi.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta bayyana ainahin wanda ya lashe zaben gwamnan Kebbi

JIBWIS ta gayyaci Dr Abdul'aziz mukabala
Mukabalar za ta gudana ne tsakanin Sheikh Idris Abdul'azi da Sheikh Dalhat Abubakar Kantana. Hoto: JIbwisFunakayeNHQJOS
Asali: Facebook

Da wa Sheikh Abdul'aziz zai gudanar da mukabalar?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin ya aika da wasikar ne karkashin cibiyar ilimi da ilimantarwa ta Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa'Ikamatis Sunnah (JIBWIS), mai shelkwata a Jos, babban birnin jihar Filato.

Ustaz Ahmad ya ce mukabalar za ta gudana ne tsakanin Sheikh Idris Abdul'azi, limamin masallacin Juma'a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, da kuma Sheikh Dalhat Abubakar Kantana.

Rahotanni sun bayyana cewa Sheikh Kantana ne ya fara aika wa Sheikh Abdul'aziz da sakon bukatar yin mukabalar a shafin Facebook, inda shi Abdul'aziz ya amince da hakan.

An shirya gudanar da mukabalar ne a babban dakin taro na Multi-purpose da ke Bauchi a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, da misalin karfe 10 na safiya, kamar yadda shafin Jibwis Funakaye ya wallafa a Facebook.

Shafin ya wallafa cewa:

Kara karanta wannan

Shari’ar Kano: ’Yan jam’iyyar NNPP sun yi ganganmin addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda

"Wannan tattaunawar za ayi ta ne bisa kyakkyawan tsari, kuma muna fatan Allah ya sa wannan mukabalar ta bada fa'ida da za ta amfanar da al'ummar musulmi."
"A yanzu dai ana jiran amsa daga Dr. Idris Abdul'aziz tare da fatan zai amince ayi wannan zaman a wurin da aka sanya wanda ba Mallakin bangarori biyun bane".

Kotu ta garkame Sheikh Abdul'aziz a gidan gyaran hali

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda kotu ta tsare babban limamin Masallacin Jumu'a Dutsen Tanshi, Dakta Idris Abdulaziz, a gidan gyaran hali.

Daily Trust ta rahoto cewa an tsare Malamin a gidan Yari ne bisa zargin yana amfani da wasu kalamai a karatuttukansa da ka iya tunzura jama'a.

Ya malamai ke kallon kalaman malamin?

A wani wa'azi da ya yi a cikin watan Ramadan, Sheikh Idris ya faɗi wasu kalamai da suka haddasa cece kuce da muhawara mai zafi tsakanin mabiya addinin Musulunci.

Wasu daga cikin Malaman Musulunci sun fassara Kalaman Sheikh Idris da miyagun kalaman batanci ga fiyayyen halinta, Annabi Muhammad (SAW).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.