Kungiyar Izalah Na Da Masallatai Da Makarantu 112,000 A Najeriya

Kungiyar Izalah Na Da Masallatai Da Makarantu 112,000 A Najeriya

  • Kungiyar da'awar addinin Islama a Najeriya ta kammala kididdigan Masallatai da makarantun dake karkashinta
  • Kwamitin da aka baiwa hakkin gudanar da wannan aiki sun gabatar da rahoton kididdigar ga shugabanta na kasa
  • Daga cikin wannan kididdiga, kungiyar ta gano akwai makarantun Islamiyya kimanin dubu arba'in

Shugaban Kungiyar Izala, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau,ya karbi rahoton aikin da ya saka mambobin kwamitin Jibwis Social Media na tattara adadin masallatan kungiyar.

Wadannan Masallatai sun hada da na juma'a, khamsu Salawati.

An gudanar da kididdigan ne a a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Ga adadin makaratu da masallatan da aka tattara:

Masallatan juma'a - 9,225

Khamsu salawat dubu - 63,409

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Makarantu - 39,727

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Jibwis
Kungiyar Izalah Na Da Masallatai Da Makarantu 112,000 A Najeriya Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

A cewar jawabin da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook tace:

"A halin yanzu kungiyar tana da bayanan duk wani limami,Na'ibi, ladani shugaban kwamitin masallaci, da shugaban makaranta, a duk fadin kasar.
Wannan lissafi ya shafi iya masallatai da makaranti mallakar kungiyar Izala ne a duk fadin kasar."

Jawabin ya kara da cewa shugaban kungiyar Sheikh Bala Lau, ya yabawa mambobin kwamitin a wannan namijin kokari da sukayi wajen bada hadin kai har aikin ya kammala cikin nasara.

A cewarsa:

"Muna yaba muku,kwarai da gaske, kuma zamu dora aikin da kuka kawo mana a kan manhajar 'google map' ta yadda duk inda mutum ya shiga a kasar nan zaka samu masallatai da makarantun izala cikin sauki akan wayar hannun ka"

Kungiyar Izalah Ta Bayyana Abinda Zatayi Da Kudin Fatun Layya N107m Da Ta Samu

A bayan mun kawo rahoton cewa Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqaamatus Sunnah watau JIBWIS ta bayyana abinda za'a yi da kudin fatun layyan da aka samu jiha bana.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

Mun kawo muku jiya cewa Izalah ta alanta samun naira miliyan dari da bakwai (₦107,704,484.25) na tattara fatun layyan shekarar 1443AH.

A baya an gina katafaren masallaci, gidan shan magani da katafaren masaukin baki a cikin birnin Abuja duk da kudaden fatun layyan da jama'a ke badawa, kungiyar ta bayyana.

Yanzu kungiyar tace za'a zuba kudaden ne wajen ginin Jami'ar kasa da kasa ta As-Salam dake jihar Jigawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel