Masu garkuwa da mutane sun bukaci N50m kafin su sako fasto da suka sace

Masu garkuwa da mutane sun bukaci N50m kafin su sako fasto da suka sace

-An sace wani babban fasto a jihar legas, a makon da ya gabata

-Masu garkuwa da mutanen sun bukaci N50m kafin su saki faston

-An sace faston akan hanyar shi ta dawowa daga wurin aiki

Masu garkuwa da mutane sun bukaci naira miliyan hamsin
Masu garkuwa da mutane sun bukaci naira miliyan hamsin

Wasu masu garkuwa da mutane, sun sace wani babban faston coci, Rev. Ekpenyong James dake Ikorodu, jihar Legas, sun tuntubi iyalan shi akan su bada N50m kafin su sake shi. Barayin sun sace shi ne akan Okurikang Junction, dake kan babbar hanyar Calabar-Itu, a makon daya gabata.

DUBA WANNAN: An gano wani kwamishina ya sace N30m

Majiyar Legit.ng tace an sace faston ne akan hanyar shi ta dawowa daga wurin aiki, mun kara samun cewar barayin sun tuntubi iyalan faston da wayar salula, inda suka bukaci a basu N50m kafin su sake, a tunanin su ya tara kudi, ganin irin ayyukan da yake yi.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, ASP Irene Ugbo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace 'yan sanda suna yin bakin kokarin su domin ganin an ceto rayuwar shi. Kwamishinan ya bayyana cewar akwai matar da suka kama wadda take tare da shi faston a lokacin da abin ya faru, yanzu haka tana hannu, abin tambayar a nan shine ya akayi ita ta kubuta.

Inda ita matar tayi kokarin kare kanta da cewar barayin sun zo sun fitar da faston ne daga mota da karfin tsiya, inda ita kuma tayi kokarin nema mafaka, abinda yasa basu kamata ba kenan.

"Kwamishinan ya tabbatar da cewar suna yin iya bakin kokarin su domin ganin sun ceto rayuwar shi."

Dama dai rashin tsaro yana daya daya daga cikin abinda yake ciwa kasar mu tuwo a kwarya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng