Bayan Zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu Ya Fadi Burin da Ya Rage Masa a Duniya

Bayan Zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu Ya Fadi Burin da Ya Rage Masa a Duniya

  • Bola Ahmed Tinubu ya na shiga takarar shugaban kasa a karon farko, ya yi nasara a babban zaben Najeriya a 2023
  • Shugaban kasan zai so ya ga sunansa a cikin littafin Guinness da ake tattara mutanen da su ka yi fice a duniya
  • Tinubu ya ce sauyin tattalin arzikin da ya kawowa jihar Legas, ya isa ya sa a rika tuna shi a cikin kundin Guinness

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Germany - Mai girma Bola Ahmed Tinubu yana da sauran buri duk da ya samu abin da yake nema na zama shugaban kasar Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu ya ce ya kamata sunan shi ya shiga cikin littafin Guinness wanda ake tattara sunayen gwarza a fagagen duniya.

Kara karanta wannan

Yadda muka sha kaye a zaben 1998 domin na ki bai wa INEC cin hanci, Obasanjo

Shugaban Najeriyan yake cewa gyare-gyaren da ya kawo ta fuskar tattalin arziki da yake mulkin Legas, abin a rubuta ne a Guinness.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a Jamus Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu a Jamus: Zan so shiga tarihin Guinness

Bola Tinubu ya ce saboda sauyin tattalin arzikin da ya kawo a jihar Legas ne bayan shekaru 16, aka zabe shi ya mulki 'yan Najeriya.

Rahotonmu ya ce shugaban kasar ya fadi wannan ne da yake jawabi a wani taron ‘yan kasuwa tsakanin Najeriya da Jamus a ketare.

Wannan ne karo na goma da kasar Jamus ta shirya wannan zama domin bunkasa kasuwanci tsakaninta da takwararta a Afrikan.

Bayan zaman Tinubu shugaban kasa, wannan ne karon farko da aka yi irin wannan taro.

Shugaba Tinubu ya na neman ajiye tarihi

A bidiyon da TVC ta wallafa a Youtube, tsohon Gwamnan na Legas ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya shiga kundin Guiness.

Kara karanta wannan

Cikakken bidiyon hirar Buhari ta farko bayan barin fadar shugaban kasa ya bayyana

Ko da ba za a shi kyautar ficen da ya yi ba, shugaban zai so sunansa ya shiga tarihi, yake cewa sai ya rubuta sunan na shi da kan shi.

Tinubu zai gyara tattalin arzikin kasa?

Shugaba Tinubu ya ce tun bayan zamansa shugaban kasa a watan Mayu, ya ke kokarin ganin ya maimaita kokarin da ya yi a Legas.

Gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya daga cikin matsi, ya na ta nadin-mukamai bayan ya shiga ofis.

Facaka da sunan Bola Tinubu?

Ana da labari cewa mutane su na zargin Gwamnatin Legas da facaka saboda za a kashe miliyoyi a sayen kaji, ganye da hotunan Bola Tinubu.

Wasu kwangiloli da Babajide Sanwo Olu ya bada ya jawo an taso Gwamnatin jihar Legas a gaba da surutai a lokacin da ake kukan rashin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng