Magudin Zabe: Jigon SDP Ya Roki Tinubu Ya Kori Shugabannin INEC, Ya Hukunta Yakubu
- Wani babban jigo a jam'iyyar SDP ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya kori shugabannin hukumar zabe ta kasar tare da gurfanar da Farfesa Yakubu
- Ben Adaji, ya ce wannan kiran ya zama dole biyo bayan yadda INEC ta gudanar da zaben jihar Kogi, zaben da ya kira shi da "fashi da tsakar rana"
- Adaji ya kuma bayyana cewa magudin zabe da karya dokokin zaben da aka yi na iya jawo tashin-tashina a tsakanin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jalingo, jihar Taraba - Jigon jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Ben Adaji, ya roki Shugaba Bola Tinubu da ya rusa shugabancin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Adaji ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jalingo, jihar Taraba, yayin da yake mayar da martani kan zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar kwanan nan.
An tafka magudin zabe a zaben jihar Kogi - Adaji
Da yake bayyana rashin jin dadinsa da yadda aka gudanar da zaben, Adaji ya bukaci da a gaggauta kama shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmood Yakubu tare da gurfanar da duk wani jami’in da ke da hannu a abin da ya kira “fashi da tsakar rana a Kogi.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata kakkausar suka, Adaji ya tabbatar da cewa, zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, ya jawo wa dimokuradiyyar Afirka abin kunya a idon duniya ba, tare da zama abin izgili ga kasar.
Dan takarar majalisar wakilan tarayya a mazabar Ankpa a zaben 2023 ya yi gargadin cewa rashin da’ar da INEC ta nuna a zaben na iya bude kofar rashin bin doka da oda a kasar nan a fakaice, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Akwai bukatar shugaban INEC , Farfesa Yakubu ya yi murabus - Adaji
Ya kara da cewa an yi magudin zabe da karya dokokin zabe a yayin gudanar da zaben jihar lamarin da ka iya jawo tashin-tashina a tsakanin al'umma.
Ya bayyana rashin jin dadinsa ga Farfesa Yakubu, yana mai jaddada cewa akwai bukatar shugaban INEC ya yi murabus biyo bayan zaben Kogi, kamar yadda jam'iyyar LP ita ma ta mika bukatar hukunta Yakubu, Channels TV ya ruwaito.
Jigon na SDP ya zargi INEC da kalamai masu cin karo da juna da kuma amincewa da sakamakon da aka samu daga wuraren da aka yi magudi da karya dokokin zabe.
Dino Melaye ya zargi APC, INEC da shirya magudin zabe a jihar Kogi
A ranar da aka gudanar da zaben jihar Kogi, Legit ta ruwaito maku yadda Dino Melaye, ya umurci jami'an jam'iyyarsu da su nuna turjiya idan INEC ta ki nuna masu tsaftatacciyar takardar rubuta sakamakon zabe.
Melaye, dan takarar gwamnan jihar Imo, ya yi zargin cewa jami'an hukumar zaben sun ki nuna wa jami'ansu takaradar rubuta sakamakon zaben don tantance wa.
Asali: Legit.ng