An Kai Farmaki Hedikwatar Rundunar Yan Sandan Jihar Adamawa, Bayanai Sun Fito
- Hedikwatar rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta fuskanci hari da sanyin safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an kwashe kusan aƙalla mintuna 30 ana jiyo ƙarar harbe-harben bindiga
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar harin ya bayyana cewa ana cigaba da bincike domin gano waɗanda suka kawo harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Wasu ƴan bindiga sun kai hari hedikwatar ƴan sandan jihar Adamawa da sanyin safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, lamarin da ya jefa mazauna birnin Yola cikin firgici.
Hedikwatar ƴan sandan tana tsakiyar Jimeta ne a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa.
Wani mazaunin birnin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an ji sautim harbe-harbe a saman iska na aƙalla mintuna 30.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me rundunar ƴan sanda ta ce kan harin?
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust aukuwar harin, amma ya ce an shawo kan lamarin.
Nguroje ya ce an daƙile harin, amma ba a san ko su waye suka kai harin ba.
Wata majiya ta ce maharan jami'an sojoji ne da suka zo ramuwar gayya, biyo bayan kashe wani jami'in soja da ƴan sanda suka yi.
Babu tabbacin cewa ko akwai hannun jami'an sojoji a harin, amma rundunar ƴan sandan ta ce ana cigaba da bincike don gano musabbabin harin da kuma waɗanda suka kai harin.
Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan takun saƙa tsakanin jami'an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) da kuma jami'an rundunar sojin saman Najeriya a Kaduna.
Gaskiya ta fito: Yadda dakarun sojoji suka daƙile harin da 'yan ta'adda suka kai wa ayarin gwamnan APC a arewa
Sufeto Janar Na Ƴan Sanda Ya Bayyana Gaban Majalisa
A wani labarin kuma, Sufeto Janar na ƴan sanda (IGP) Kayode Egbetokun tare da sauran manyan hafsoshin tsaro sun bayyana a gaban majalisar tarayyar Najeriya.
Manyan shugabannin tsaron na ƙasa sun bayyana ne a gaban majalisar tarayyar domin tattauna halin tsaron da ake ciki a ƙasa, bayan da farko sun ƙi zuwa inda suka turo wakilai.
Asali: Legit.ng