Shugabannin Sojoji da Sufetan Yan Sanda Sun Bayyana Gaban Majalisar Tarayya Don Tattauna Tsaro

Shugabannin Sojoji da Sufetan Yan Sanda Sun Bayyana Gaban Majalisar Tarayya Don Tattauna Tsaro

  • Majalisar tarayyar Najeriya ta gana da manyan hafsoshin tsaro tare da sufetan 'yan sanda a zauren majalisar da ke Abuja, a ranar 21 ga watan Nuwamba
  • Ganawar na zuwa ne bayan da majalisar tarayyar ta soki hafsoshin tsaron kan aiko wakilai a majalisar maimakon zuwa da kansu a ranar Ahamis din da ta gabata
  • Tattaunawar za ta shafi hanyoyin da za a kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Manyan hafsoshin tsaro da sufeto janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, sun bayyana gaban majalisar wakilan tarayyar Najeriya.

Shuwagabannin sojojin sun hada da babban hafsan tsaro (CDS), Janar Christopher Musa; babban hafsan sojoji (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Yadda dakarun sojoji suka daƙile harin da 'yan ta'adda suka kai wa ayarin gwamnan APC a arewa

Majalisar Tarayyar Najeriya
Shugabannin tsaro da sufetan 'yan sandan sun bayyana gaban majalisar ne don tattauna batutuwan tsaron Najeriya. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisar tarayyar ta soki hafsoshin tsaro

Sai kuma babban hafsan sojan sama (CAS), Air Marshal Hassan Abubakar, da shugaban rundunar sojojin ruwa (CNS), Vice Admiral Emmanuel Ogalla, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shigar da su cikin zauren majalisar domin muhawara kan lamuran tsaro da misalin karfe 11:26 na safe.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta suki shugabannin tsaro a ranar Alhamis din da ta gabata kan tura wakilai, wadanda majalisar tarayyar ta ki saurara.

Hafsan sojin ruwa ya gabatar da babbar bukata gaban majalisar tarayya

Kafin taron zartarwar, shugabannin hafsoshin da IGP sun yi jawabi bi-da-bi inda suka bayyana kokarin da ake yi na magance matsalar tsaro a kasar, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, ya bukaci majalisar dokokin kasar ta sa baki wajen inganta fasar leken asiri don sa ido a manyan hanyoyin ruwa, koguna, da sauran wuraren da ke bayan gabar teku inda 'yan ta'adda ka iya boyewa.

Kara karanta wannan

An sake kama hatsabibin dilallin kwayoyi shekaru 7 bayan tserewarsa daga gidan yari a Abuja

A cewarsa, idan aka yi haka, za a rika sa ido a kan satar mai, fasa bututun mai, da kuma masu tace mai ba bisa ka’ida ba.

Majalisar dattawa ta gayyaci hafsoshin tsaro kan sace daliban jami'a

A wani labarin da Legit Hausa ta kawo maku, kun ji majalisar dattawa, a ranar Alhamis, ta yanke shawarar gayyatar dukkan shugabannin jami’an tsaro saboda karuwar garkuwa da daliban jami’a a sassan Najeriya.

Daily Trust ta ce hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua (Katsina ta tsakiya) ya gabatar wanda ya jawo hankalin sauran abokan aikinsa a zaman yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel