Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya Christopher Musa Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya Christopher Musa Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana

  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke yadawa na cewa babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa ya rasu
  • Birgediya Janar Tukur Gusau, daraktan yada labarai na DHQ, ya fitar da wata sanarwa a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, inda ya tabbatar da cewa Janar Musa yana nan da ransa
  • Janar Gusau ya soki rahoton a matsayin abin takaici, wanda bai dace ba mai cike da rashin gaskiya, inda ya bayyana cewa jaridar da ke da alhakin wannan jita-jitar ta janye batun tare da neman afuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ƙaryata labarin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa na cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Gwabin Musa ya rasu.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Yadda dakarun sojoji suka daƙile harin da 'yan ta'adda suka kai wa ayarin gwamnan APC a arewa

Wani rahoto da aka fitar dai ya yi iƙirarin cewa shugaban hafsan tsaron na ƙasa ya rasu.

Christopher Musa yana a raye
DHQ ta musanta rasuwar babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Christopher Musa Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Sai dai a wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau, daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaro ya fitar a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa hafsan tsaron yana nan cikin ƙoshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Gusau ya ce rahoton abin takaici ne, wanda bai dace ba mai cike da rashin gaskiya.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hankalin hedikwatar tsaro ya kai kan wani labari mara daɗi da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa tana zargin cewa babban hafsan hafsoshin Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya rasu a jiya."
"Domin bayyana yadda abun yake, Janar CG Musa, yana raye kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Babban hafsan hafsoshin tsaron wanda ya dawo daga wani aiki a ƙasar waje, ya cigaba da aiki tare da ƙarin himma domin cigaba da salon shugabancinsa domin ciyar da rundunar sojin Najeriya gaba.”

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

Raɗe-raɗin rasuwar Christopher Musa: Jaridar ta nemi afuwa

Janar Gusau ya ce jaridar ta yanar gizo da ta bayar da rahoton rasuwar da ake yaɗawa ta janye shi.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa, jaridar ta nemi afuwa ga CDS, iyalansa da kuma rundunar sojojin Najeriya.

Rundunar Soji Ta Samu Farfesa a Karon Farko

A wani labarin kuma, rundunar sojojin Najeriya ta samu Farfesa a karon farko a cikin tarihinta.

Laftanal-Kanal Abubakar-Surajo Imam na Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya (NDA) ya samu ƙarin girma zuwa matsayin Farfesa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng