Duk Da Mijina Yana Lakada Min Duka, Bana Son a Raba Auren Mu, Mata Ta Fadawa Kotu a Kaduna
- Wani magidanci ya gurfana gaban kotun shari'a da ke Magajin Gari Kaduna bisa zarginsa da lakadawa matarsa da yaransu dukan tsiya
- Magidancin ya shaidawa kotun cewa yana dukan matar da yaran ne kawai idan suka aikata laifi, kuma yana yin hakan don gyara masu tarbiya
- Alkalin kotun, ya bukaci magidanci ya dau alwashin daina cin zarafin matar, tare da ba shi shawarwarin hanyar da ya kamata ya bi don tarbiyar yaran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Wani mahaifi mai ‘ya’ya hudu Lukman Soladoye, a ranar Talata, ya bayyana a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna bisa laifin dukan matarsa Kemi Soladoye da ‘ya’yansu hudu.
Soladoye ya ce ya lakadawa matarsa da ’ya’yansa duka da ya ke yi, yana yi ne don gyaran tarbiyarsu a lokutan da suka yi kuskure inda ya ce yana kaunar iyalinsa kuma yana son su yi kyakkyawar rayuwa.
Matar na son mijinta duk da yana dukan ta, ta roki kotu sasanci
Tun da farko dai mai shigar da karar ta bakin lauyanta B.A Tanko ta ce ta na son a raba auren ne saboda cin zarafi da mijin ke yi mata amma daga baya ta sauya ra’ayinta ta na neman sasanci da mijin nata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta roki kotun da ta gargadi wanda take karar da ya daina cin zarafinta da ‘ya’yansu, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Alkalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahman, ya tambayi wanda ake kara ko zai yi alkawarin daina dukan matarsa da ‘ya’yansa, shi kuma wanda ake kara ya ce zai daina dukan matar amma banda ‘ya’yan.
Yadda ake tarbiyyantar da iyalinka, alkali ya ba magidanci shawara
Abdulrahman ya ce:
“Idan matarka ta yi maka wani laifi, ka yi magana da ita kuma ka nuna bacin ranka, amma bai kamata ka yi wa matarka duka ba.
“Game da ‘ya’yan ku kuwa, ba duka ba ne kawai hanyar da za ku gyara yaro, ku nuna so da kauna ga yaranku, ku yi musu addu’a, ku yi masu nasiha,”
Jaridar Tribune ta rahoto Alkalin na cewa kotun za ta ci gaba da sanya ido kan halayen wanda ake karar sannan ya bukaci mai karar da ta kai kara kotu idan mijin ya sake cin zarafinta.
Kotu ta umurci magidanci ya karbi dan da matarsa ta haifa
An samu takaddama mai zafi tsakanin wani magidanci da tsohuwar matarsa a wata kotun shari'a da ke Kano, bayan matar ta haihu kuma ta ce dan na shi ne, Legit Hausa ta ruwaito.
Sai dai magidancin ya ki karbar yaron, yana ikirarin dan da ta haifa ba nashi bane, sakamakon gwajin da aka yi a asibiti tun bayan kwanaki 16 da zuwanta gidansa.
Alkalin kotun Khadi Abdullahi, ya ba mutumin umurnin karbar yaron kasancewar ya gaza kawo hujjar ganin matar da wani.
Asali: Legit.ng