Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa maigida duka

Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa maigida duka

- Wani magidanci, Adebayo ya yi karar matarsa a kotu yana neman a datse igiyar aurensu saboda matar da yaransu suna dukansa

- Matarsa, Sherifat bata musanta cewa ita da yaranta sun doke mijin ba amma ta ce shi ya fara neman rikici ya yaga mata kaya

- Alkalin kotun ya yi tir da batun dukan mai gidan ya raba auren sannan ya gargadi yaran game da daga hannu su doki mahaifinsu

Wani dan kasuwa, Abideen Adebayo, a ranar Talata ya bukaci wata kotu da ke Ile-Tuntun ta raba aurensa na shekaru 27 da matarsa Sherifat.

Ya shaidawa kotu cewa matarsa Sherifat da yaranta biyu cikin hudu da suka haifa su kan taru su lakada masa duka don haka ya ke son a raba auren.

Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa miji duka
Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa miji duka. HotoL @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

"Sherifat ba ta da biyayya ga neman rikici kuma ta dade tana nuna min cewa ba za ta iya kula da gida ba.

"Saboda magiyar ta, Sherifat ta bar gida na watanni shida da suka shude amma ta kan zo a lokacin kirsimiti.

"A ranar 25 ga watan Disambar 2020, Sherifat ta zuga manyan yaran mu biyu su taru su min duka.

"Sai da na kira yan sanda aka kama su," in ji shi.

Mai shigar da karar ya kuma ce matarsa ta saba zuwa wurin aikinsa ta tada rikici.

Mr Adebayo ya nuna wa kotun bidiyon rashin mutuncin da aka masa watan Disambar bara.

KU KARANTA: Alƙali ya bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai

A bangarenta, Sherifat ba ta musanta zargin da mijinta ya yi ba amma ta shaidawa kotun cewa mijin baya kulawa da ita da yaranta.

Ta ce baya biyan kudin makarantar yara sannan ya lalata mata kekunan dinki guda hudu.

"Adebayo ne ya fara kai min hari da na zo gidansa a ranar 25 ga watan Disamban 2020 ta hanyar yaga min kaya," in ji ta.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Henry Agbaje ya yi Allah wadai dukan da yaran suka yi wa mahaifinsu ya kuma hane su da yin hakan a gaba.

Agbaje ya raba auren ya bawa yaran zabin su zauna da duk wanda suke so tunda sun girma, ya kuma ce Adebayo ya cigaba da kulawa da su.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel