Innalillahi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Fama da Ciwon Zuciya
- Tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Ondo, Manjo Janar Ekundayo Opaleye ya riga mu gidan gaskiya a Abeokuta
- Marigayin ya mulki tsohuwar jihar Ondo tsakanin shekarar 1986 zuwa 1987 a mulkin Ibrahim Badamasi Babangida
- Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tura sakon ta'aziya ga iyalan mamacin inda ya yi addu'ar ubangiji ya gafarta masa kura-kuransa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun- Tsohon gwamnan jihar Ondo na mulkin soja, Manjo Janar Ekundayo Babakayode Opaleye ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne a Abeokuta da ke jihar Ogun a yau Asabar 18 ga watan Nuwamba dalilin ciwon zuciya, cewar Leadership.
Wasu mukamai marigayin ya rike kafin rasuwarshi?
Opaleye shi ne ya rike mukamin gwamnan tsohuwar jihar Ondo da Ekiti a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida daga 1986 zuwa 1987.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ekundayo ya karbi mukin ne a hannun marigayi Mike Akhigbe kafin mika mulki ga Bode George.
Kafin rasuwar marigayin, shi ne Balogun na Erunmu, Owu na Abeokuta babban birnin jihar Ondo, Daily Trust ta tattaro.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babbar rashi ga jihar da ma kasa baki daya.
Wane martani Gwamna Abiodun ya yi kan rasuwar?
Abiodun ya bayyana irin gudunmawar da ya bayar a rundunar soji da kuma lokacin da ya ke gwamna a matsayin abin da ba za a taba mantawa ba.
Ya ce:
"Ba za mu taba mantawa da irin gudummawar da Opaleye ya bayar ba a Najeriya da ma rundunar sojin kasar.
"Haka nan gudummawar da ya bayar a lokacin mulkin jihar Ondo ba zai misaltu ba, wannan babban rashi ne ga kasar baki daya.
"Mu na isar da sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da kuma fatan samun hakurin jure wannan babban rashi."
Mace Manjo Janar ta farko ta rasu
A wani labarin, mace ta farko da ta taba zama Manjo Janar ta farko, Aderonke Kale ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiya Kale ta rasu ne a birnin Landan a ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba bayan fama da doguwar jinya.
Asali: Legit.ng