Yan Ta'adda Fiye da 60 Sun Mutu Yayin da Sabon Yaki Ya Barke Tsakanin Boko Haram da ISWAP
- Fada ta barke tsakanin mayakan Boko Haram da kuma 'yan kungiyar ISWAP wanda ya yi ajalin mayaka 60 a jihar Borno
- Fadan ya faru ne a tsibirin Tumbum Ali da ke karamar hukumar Marte na jihar inda lamarin ya yi sanadin mutuwar wani kwamanda
- Rahotanni sun tabbatar da cewa fadan bai rasa nasara da kisan mayakan ISWAP da bangaren Bakura Buduma su ka yi a 'yan kwanakin nan a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - Mayakan Boko Haram da ISWAP sun bai wa hamata iska yayin da fada ya barke a tsakaninsu.
Yayin fadan, mayakan da dama sun rasa rayukansu daga ko wane bangare inda wani babban kwamanda ya mutu a jihar Borno.
'Babu ilimi a ciki', Ganduje ya bayyana hanya daya tak da su ka bi wurin nakasa Kwankwaso, Abba Kabir
Yaushe lamarin ya faru da ya yi ajalin Boko Haram/ISWAP?
ZagazOlaMakama ya bayyana a shafin Twitter cewa fadan ya barke ne a tsakaninsu a tsibirin Tumbum Ali da ke karamar hukumar Marte.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne bayan kai harin ramuwar gayya da ISWAP su ka yi kan bangaren Buduma da su ka kashe 'yan kungiyar.
TheCable ta tattaro cewa an tarwatsa jiragen ruwa shida na bangaren Bakura Buduma da sauran kayayyakinsu.
Mayakan Boko Haram, ISWAP nawa su ka mutu?
Har ila yau, mayaka akalla 60 ne aka kashe yayin fadan wanda har zuwa yanzu ana kan fafatawa.
Wannan ba shi ne karon farko ba da matakan ke bai wa hammata iska a tsakaninsu saboda wasu dalilai da su ka shafi mamayar wurare da shugabanci.
A kwanakin baya ma irin haka ta faru inda mayakan ko wane bangare da dama su ka rasa rayukansu sanadin rikicin.
Sojoji sun hallaka kwamandan 'yan bindiga Kebbi
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya sun yi ajalin wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi jama'a a jihar Kebbi.
Marigayin mai suna Mainasara ya shahara wurin kai hare-hare wanda kuma kwamanda ne a yankin da ke fama da rashin tsaro.
Yankin Arewa maso Yamma na fama da rashin tsaro na 'yan bindiga musamman a yankunan karkara inda aka yi asarar rayuka da dama
Asali: Legit.ng