Satar Mazakuta: Kotu Ta Tura Mutum 2 da a Ke Zargi Zuwa Gidan Gyaran Hali

Satar Mazakuta: Kotu Ta Tura Mutum 2 da a Ke Zargi Zuwa Gidan Gyaran Hali

  • Wasu matasa biyu sun gurfana a wata kotun majistare da ke birnin Port Harcourt a jihar Rivers kan zargin lakaɗawa wani tsoho da matarsa duka
  • Matasan dai sun zargi tsohon ne da laifin sace mazakutar ɗaya daga cikinsu wanda hakan ya sanya suka yi masa dukan tsiya
  • Alƙalin kotun ya bayar da umarnin a tura su zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a cigaba da sauraron ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Kotun Majistare ta II da ke zamanta a Port Harcourt, a ranar Juma’a ta tasa keyar John Shadrack mai shekara 22 da William Isaiah, mai shekara 33, zuwa gidan gyaran hali bisa cin zarafin Mista Felix Tuoyo, mai shekaru 70, kan zargin satar mazakuta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

An tsare mutanen ne bisa tuhumar da ake musu kan laifuka biyu na haɗa baki da kuma cin zarafi, cewar rahoton Daily Nigerian.

Kotu ta tura mutum biyu gidan gyaran hali
Kotu ta tura mutum biyu gidan gyaran hali kan zargin cin zarafin wani tsoho Hoto: tribune.com
Asali: UGC

Jami'i mai shigar da ƙara, Insfeta M. Ebirie, ya shaida wa kotun cewa a ranar 24 ga Oktoba, a SPAR Shopping Mall da ke Port Harcourt, waɗanda ake tuhumar sun ci zarafin Tuoyo da matarsa, Susan, bisa zargin cewa dattijon ya sace mazakutar Shadrack.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ake tuhumarsu da shi?

Ebirie ya bayyana cewa waɗanda ake tuhumar da waɗanda suka aikata laifin tare da suka tsere yanzu, sun haɗa baki ne wajen aikata laifin wanda ya saɓa wa sashe na 516 (A) na kundin laifuffuka na dokar jihar Rivers.

Ya ce waɗanda ake tuhumar da waɗanda suka tseren, sun ci zarafin mutanen biyu ba bisa ƙa’ida ba ta hanyar yi musu dukan tsiya wanda hakan ya haifar da illa ga jiki da kuma karaya a ƙafar hagu ta matar, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Innalillahi, Wani babban Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

A cewarsa, wannan laifi ne da ake hukuntawa a ƙarƙashin sashe na 355 na kundin laifuffuka, dokokin tarayya kamar yadda ya dace a jihar Ribas.

Bayan sauraron ƙarar, babban alƙalin kotun, R. N. Ibanibo, ya bayar da umarnin a cigaba da tsare waɗanda ake ƙara a gidan gyaran hali sannan ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba domin cigaba da sauraron ta.

Matasa Sun Far Wa Ɗan Achaba Kan Satar Mazakuta

A wani labarin kuma, wasu fusatattun matasa sun far wa wani ɗan Achaɓa a birnin tarayya Abuja kan zargin satar mazakuta.

Matasan dai sun farmaki ɗan Achaɓan ne bayan fasinjan da ya ɗauka ya bayyana cewa bai ga mazakutarsa ba bayan ya sauka daga babur ɗinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng