Rundunar Yan Sanda Ta Yi Martani Kan Rahotannin 'Satar Mazakuta' a Borno

Rundunar Yan Sanda Ta Yi Martani Kan Rahotannin 'Satar Mazakuta' a Borno

  • Hukumar 'yan sanda ta karyata jita-jitar da mutane ke yadawa a jihar Borno, na cewar ana sace wa maza mazakuta da zaran sun yi musabaha da bakon fuska
  • Hukumar ta ce binciken asibiti ya tabbatar da cewa wannan zargi karya ce tsagwaronta, da hakan ta ke rokon al'ummar jihar su watsar da irin wannan jita-jitar
  • Haka zalika, hukumar ta bayar da lambobin da mutane za su tuntube ta idan an ga wani abu da ba'a yarda da shi ba, ko akai rahoto kai tsaye ga ofishin hukumar mafi kusa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Maiduguri, jihar Borno - Hukumar 'yan sanda ta jihar Borno, ta karyata jita-jitar da ake yada wa a kafofin sada zumunta na zamani, na cewar ana satar mazakuta a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

A cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar (PPRO), ASP Nahum Daso Kenneth, a ranar Talata a Maidguri, rundunar ta ce ta karbi korafe korafe kan jita-jitar da ake yada wa na bacewar mazakutar maza da zaran sun yi musaba da bakin fuska.

Jami'in hukumar 'yan sanda
Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda reshen jihar Borno, ya ce batun satar mazakuta karya ce tsagwaron ta Hoto: nk_daso
Asali: Twitter
"Duk wadanda suka yi ikarin sace masu mazuka an kai su asibiti, kuma rahoton gwaji ya nuna zargin bacewar mazakutar shaci fadi ce kawai, kasancewar mazakutarsu na nan, kuma tana aiki."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A kan hakan, rundunar na sanar da al'umar jihar Borno da su kwantar da hankulansu, tare da bin doka da oda, da kuma yin watsi da irin wannan jita-jitar da ka iya tayar da zaune-tsaye a jihar."

Sanarwar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, ta ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Hukumar Hisba za ta aurar da Murja Kunya da sauran 'yan TikTok na Kano

"Kazalika, rundunar na amfani da wannan damar wajen kira ga al'umar jihar da su ci gaba da harkokin gabansu ba tare da wata fargaba ba, da kuma sanar da rundunar faruwar wani abu wanda basu yarda da shi ba."

Rundunar ta sanya lambobin da jama'a za su tuntuba don bayar da rahoto, ko kuma zuwa wani ofishin hukumar da ke mafi kusa. Lambobin da hukumar ta bayar su ne:

  1. 09025437854
  2. 08068075581

An lakada wa fasto dukan tsiya akan zargin satar mazakuta

A wani labarin makamancin wannan, kun ji cewa wani fasto da hadiminsa a cocin New Generation sun tsallake rijiya ta baya-baya kan zargin batar mazakuta a jihar Benue.

Ana zargin faston ne bayan wani matashi ya rasa mazakutarsa a unguwar New Layout da ke Kanshio a bayan garin Makurdi babban birnin jihar, Legit ta tattaro.

Matasa sun yi ajalin wani Alhaji kan zargin satar mazakuta

A wani labarin, wasu fusatattun matasa sun yi ajalin wani Alhaji Tijjani Yakubu a birnin Abuja kan zargin satar mazakuta, Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ofishin jakadacin Kanada ya dakatar da ayyukansa a Najeriya, ya fitar da gargadi

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin yawar satar mazakuta ta yi yawa a tsakanin al’ummar Najeriya.

A kwanakin baya, Sanata Shehu Sani ya gargadi jama’a kan daukar doka a hannu inda ya ce sharrin matsafa ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel