Shari'ar Gwamnan Kano: NNPP Ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotun Koli Tare Da Matakin Na Gaba
- Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta ce ba ta gamsu da hukuncin kotun daukaka kara na korar Abba daga kujerar gwamnan jihar Kano ba
- NNPP ta ce za ta garzaya kotun koli don neman hakkin da aka kwace mata, tare da fatan kotun kolin za ta yi mata adalci akan hakan
- A ranar Juma'a ne kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun kararrakin zabe na ayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bayyana bakin cikinta game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, da ta kori gwamnan Kano, Abba Yusuf.
Jam'iyyar ta ce za ta binciki duk wata hanya ta doka da za ta kwato mata hakkinta.
Jami'in bincike na jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ya shaidawa jaridar The Nation cewa jam’iyyar za ta tunkari kotun koli da imanin cewa za ta samu nasarar kwato hakkinta da aka kwace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke, wanda ta soke zaben Yusuf, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Har yanzu muna da damar kwato hakkin mu - NNPP
Kotun ta kuma ta tabbatar da dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ya ce jam'iyyar NNPP tana da yakinin cewa kotun koli za ta tabbatar da zaben Engr Yusuf, inda ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar da su kwantar da hankalinsu tare da baiwa jam'iyyar damar daukar matakan da suka dace don kwato mata hakkinta.
Bangaren jam’iyyar da ke biyayya ga wanda ya kafa ta ya kuma yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, yana mai cewa jam’iyyar har yanzu tana da damar da za ta kwato hakkinta a kotun koli.
Kotun koli zata yi abin da ya dace - NNPP
Shugaban kungiyar na kasa Dr. Agbo Major ya shaidawa jaridar The Nation cewa jam’iyyar bata ji dadin hukuncin kotun daukaka kara ba.
Sai dai ya ce jam'iyyar na sa ran bangaren shari’a ta hanyar kotun koli ta fanshi kanta ta hanyar yin abin da ya dace.
Kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Abba Kabir na jihar Kano
Idan ba ku manta ba, kotun ɗaukaka kara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Kwamitin alkalan kotun ya tabbatar da hukuncin da kotun zabe karkashin jagorancin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay ta yanke wanda ya tsige Abba ranar 20 ga watan Satumba.
Bayan haka ne Kotun ta bayyana Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da ƙuri'u mafi rinjaye, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Asali: Legit.ng