Tashin Hankali Yayin da Mutane Suka Mutu Bayan ’Yan Bindiga Sun Haddasa Fada Tsakanin Kauyuka

Tashin Hankali Yayin da Mutane Suka Mutu Bayan ’Yan Bindiga Sun Haddasa Fada Tsakanin Kauyuka

  • An rasa rayuka da dama a jihar Sokoto bayan ‘yan bindiga sun haddasa fada tsakanin kauyuka
  • Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai wata mata mai shayarwa tare da jaririnta wanda aka yi ajalinsu
  • Bayan binne wadanda suka mutun ne kuma wasu matasa da ‘yan sa kai suka kai farmaki kauyukan Fulani da ke kusa

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto – Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan fada ya barke dalilin harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Daily Trust ta tattaro cewa kauyuka hudu ne aka kai musu farmaki tsakanin ranar Lahadi zuwa Laraba inda aka hallaka mutane bakwai.

'Yan bindiga sun haddasa fada tsakanin kauyukan jihar Sokoto
An rasa rayuka bayan haddasa rigima da 'yan bindiga suka yi a Sokoto. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Facebook

Mutane nawa suka rasa ransu?

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi barna a Kaduna, sun sungume Hakimi a sababbin hare-hare

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai mace mai shayarwa da ‘yarta inda aka kona su har lahira a cikin mota, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maharan har ila yau, sun raunata mutane da dama yayin da su ka sace wasu mutane da suka hada da mata da yara.

Kauyukan da aka kai hare-haren sun hada da Gidan Kakale inda aka sace mutane biyar sai Ruwa Wuri inda aka hallaka direban mota tare da kona su.

Mene dalilin rikicin?

Sauran sun hada da kauyen Alele Sutti da kuma kauyen Alkasu inda suka hallaka mutane hudu da sace wasu mutane 17, cewar Tori News.

Wani mazaunin Tangaza ya bayyana cewa ana gama binne matar da jaririnta, sai wasu matasa da ‘yan sa kai suka kai farmaki kauyukan Fulani da ke kusa.

Rahotanni sun tabbatar da hallaka mutane da raunata da dama yayin kai harin tsakanin kauyukan.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka sace ma'aikacin CBN da wasu 2 suna neman N10m kudin fansa

Majiyar ta tabbatar da cewa hare-haren sun yi yawa ne saboda yadda kauyukan ke kusa da dajin Tsauna da Kuyan da ta ratse Jamhuriyar Nijar.

Har ila yau, majiyar ta tabbatar da cewa mafi yawan maharan da suka addabi yankunan ‘yan kasashen ketare ne.

Sojoji sun hallaka Mainasara a jihar Kebbi

Kun ji cewa, sojoji sun yi ajalin wani kasurgumin dan bindiga a jihar Kebbi bayan artabu.

Dan bindigan wanda kuma kwamandan ‘yan bindigan ne mai suna Mainasara ya rasa ransa bayan wani farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.