Gwamnan PDP Ya Yi Wa Ma'aikata Karin Dubu 25, Ya Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi

Gwamnan PDP Ya Yi Wa Ma'aikata Karin Dubu 25, Ya Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi

  • Gwamnatin jihar Enugu ta ware makudan kudade ga ma'aikata don rage musu radadin cire tallafin mai a kasar
  • Gwamna Mbah Peter na jihar Enugu ya amince da biyan makudan kudaden da suka kai 10 zuwa 25 don saukaka wa al'umma
  • Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Alhamis 16 ga watan Nuwamba a shafinsa na Twitter

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya faranta wa ma'aikatan jihar bayan musu gagarumar kyauta.

Mbah ya amince da kyautar naira dubu 10 zuwa dubu 25 ga ma'aikatan inda ya yi alkawarin tattauna batun mafi karancin albashi, Legit ta tattaro.

Gwamna Mbah na PDP ya gwangwaje ma'aikata da kyautar kudade a jihar
Ma'aikata na murna yayin da Gwamna Mbah ya mu su goma ta arziki. Hoto: Peter Ndubuisi Mbah.
Asali: Twitter

Mene Gwamna Mbah ke cewa kan ma'aikata?

Kara karanta wannan

Almundahanar N200m: Gwamnatin Filato ta fara bincikar tsofaffin ma'aikatan hukumar alhazai

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafin Twitter a yau Alhamis 16 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin jefa walwala a zukatan ma'aikatan jihar tare da inganta ayyukansu.

Ya kara da cewa akwai wasu tsare-tsare da ya shirya wa 'yan jihar don ganin sun samu walwala ganin yadda rayuwa ta yi tsada a wannan karo.

Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin mai da aka yi a kasar wanda ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa.

Wane alkawari Gwamna Mbah ya yi?

Gwamna Mbah ya ce:

"Na shirya inganta rayuwar al'umma da kuma dakile talauci baki daya.
Mun ware naira biliyan 1.5 don walwalar jama'a da kuma inganta harkar ruwa da tsaftace muhalli."

Wannan na daga cikin kokarin gwamnatin na rage wahalar ma'aikata saboda cire tallafi.

Mbah ya kara da cewa zai bayar da mafi karancin albashi har naira dubu 100 ga ma'aikatan jihar.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: "Mun kama waɗanda suka jibgi shugaban NLC" NSA ya aike da sako ga kungiyoyin kwadago

Gwamna Dare ya sanya dokar ta baci a harkar ilimi

A wani labarin, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimin jihar baki daya.

Dare ya ce matakin ya zama dole ganin yadda tsohuwar gwamnati ta lalata harkar ilimi gaba daya.

Gwamnan har ila yau, ya kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.