Kano: DSS Ta Gurfanar da Dan Boko Haram Da Ya Kai Hari a Masallaci a 2014, An Samu Matsaya
- Hukumar DSS ta sake gurfanar da dan kungiyar Boko Haram a gaban kotu kan harin bam a 2014
- Ana zargin Husseni Isma'il da kisa harin bam a babban masallacin Kano a 2014 da ya yi ajalin mutane 81
- Harin wanda shi ne mafi muni da kungiyar ta kai ya yi sanadin raunata mutane akalla 150
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta sake gurfanar da Husseni Isma'il da ake zargi da hannu a harin bam kan masallacin Kano.
Ana zargin Ismail wanda aka fi sani da Maitangaran da kisa harin kan babban masallacin a shekarar 2014, cewar TheCable.
Mene lauyan DSS ke cewa kan wanda ake zargin?
Harin ya yi sanadin mutuwar mutane 81 da jikkata fiye da 150 a shekarar 2014 a jihar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta DSS ta gurfanar da wanda ake zargin ne a babbar kotun Tarayya da ke Abuja.
Lauyan hukumar ta DSS, E. Aduda ya ce a jiya Laraba DSS ta sake sabon korafi kan wanda ake zargi don kare kansa.
Aduda ya ce Maitangaran ya tabbatar da cewa shi dan kungiyar Boko Haram ne, wacce ta saba wa dokokin kasa ta shekarar 2013.
Lauyan wanda ake zargi, Peter Dajang ya ce bai kamata kotun ta ci gaba da shari'ar ba saboda an saba ka'idojin kotun.
Martanin lauyan wanda ake zargi
Dajang ya kara da cewa kotun a ranar 6 ga watan Disamba ta umarci dauke wanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Ya ce umarnin kotun shi ne bai wa lauyoyinsa da iyalansa daman ganawa da shi, amma DSS ta ci gaba da rike shi har zuwa yanzu.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran shari'ar zuwa 25 ga watan Janairun 2024 kan umarnin kotun.
Har ila yau, ya sanya 7 ga watan Faburairu a matsayin ranar sauraran shari'ar kan wanda ake zargi.
An tsaurara tsaro kan hukuncin kotun Kano
A wani labarin, yayin da ake shirin yanke hukunci kan zaben Kano, an baza jami'an tsaro.
Har ila yau, jihar Plateau da ake ci gaba da shari'ar, an tsaurara tsaro a fadin jihar don kauce wa tashin hankali.
Asali: Legit.ng