Miyagun Ƴan Bindiga Sun Halaka Babban Malamin Addinin da Suka Sace Bayan Karɓar Kuɗin Fansa a Kogi
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka wani babban fasto a jihar Kogi bayan sun yi garkuwa da shi
- Ƴan bindiga waɗanda suka halaka fasto David Fasto sun dai salawantar da ransa ne bayan sun karɓi N1m a matsayin kuɗin fansa
- Mutuwar faston na cocin ECWA dai ta ƙara sanya firgici a tsakanin jama'ar cocinsa da mutanen jihar kan yawan ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kashe wani malamin cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) Fasto David Musa a jihar Kogi.
Jaridar PM News ta kawo rahoto cewa an kashe shi ne a daren ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba bayan da ƴan bindigan suka karɓi kuɗin fansa daga iyalansa har Naira miliyan daya.
Labarin mutuwar faston dai an bayyana shi ne a dandalin cocin na manhajar WhatsApp a safiyar ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, rahoton National Daily ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gajeren saƙon yana cewa:
"Cike da takaici amma da miƙa wuya gaba ɗaya ga ikon Allah, na rubuto don sanar da ku cewa waɗanda suka yi garkuwa da ɗan uwanmu Fasto Musa David, sun kashe shi bayan karɓar kuɗin fansa naira miliyan ɗaya a daren jiya. Mu sanya ƴan uwansa, coci da DCC cikin addu'o'in mu a wannan lokaci mai matuƙar wahala."
Yaushe aka sace faston?
Labarin sace faston dai ya bayyana ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba lokacin da ake tsaka da gudanar da zaɓen gwamnan Kogi. An dai yi garkuwa da faston ne a kusa da yankin Obajana.
Fasto David a baya ya kasance mai kula da cocin ECWA Bishara, a Ajaokuta. Mummunan kisan gillar da aka yi masa ya ƙara sanya firgici a tsakanin jama'ar cocinsa da ma jihar baki ɗaya.
Idan dai ba a manta ba, titin Lokoja/Obajana/ Kabba ya zama abin tsoro a cikin ƴan kwanakin nan.
Ƴan bindiga dai na ci gaba da gudanar da ayyukansu akai-akai akan hanyar, inda suke yin garkuwa da mutane tare da halaka su.
A watan Satumba, wani Manjo na soja yana cikin mutum 26 da aka sace a Aiyegunle Igun, mai tazarar kilomita kaɗan daga garin Kabba. Wasu daga cikinsu sun kuɓuta bayan mako guda da aka yi garkuwa da su. Har yanzu dai ba a san makomar wasu ba.
Ƙaramin Yaro Sace Ƴar Shekara 5
Wani labarin kuma, wani ƙaramin yaro mai shekara tara a duniya ya yi garkuwa da wata ƙaramar yarinya ƴar shekara biyar a jihar Bauchi.
Yaron wanda Almajiri ne ya kuma kira mahaifin yarinyar inda ya buƙaci da a ba shi kuɗin fansa har naira miliyan biyar.
Asali: Legit.ng