“Ina Yawan Ganinsa a Mafarki”, Matashin da Ya Kashe Mahaifinsa a Kaduna Ya Fadi Dalili
- Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta yi holen wani matashi mai shekaru 20 bisa zarginsa da kashe mahaifinsa yana tsakiyar barci
- Matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa, kuma ya bayyana cewa ya kashe mahaifin ne saboda yana yawan ganinsa a mafarki
- Ya ce mahaifin na zuwar masa a suffar tsuntsu tare da kokarin halaka shi, shi ya sa ya dauki matakin sheke shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zangon Kataf, jihar Kaduna - Ana zargin wani matashi mai shekaru 20 da haihuwa, David Felix, da laifin kashe mahaifinsa a ranar 30 ga watan Satumba, a kauyen Madakiya da ke karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya dauki matakin kashe mahaifin ne bayan da ya yi ikirarin cewa mahaifin nasa ya kan bayyana a mafarkin sa.
A cewar sa, mahaifin na zuwar masa a matsayin wani tsuntsu da fuskar dan Adam kuma yakan yi kokarin kashe shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matashin ya kashe mahaifinsa
Jaridar Vanguard ta ruwaito wanda ake zargin ya amsa tambayoyi daga manema labarai a rundunar ‘yan sandan jihar, inda ya amsa laifin sa, ya yi nadamar matakin da ya dauka.
Ya ce ya buga wa mahaifin nasa tabarya a lokacin da ya ke barci, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan, wanda ya yi holen wanda ake zargin, ya ce za a gurfanar da matashin gaban kotu bayan kammala bincike.
Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe
Wani mutumi mai shekaru 32 a duniya ya kashe mahaifinsa a ranar Asabar a kauyen Zange da ke karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe a kan gona, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
A cewar wata majiya, yaron mai suna Haruna Buba, ya aikata kisan ne biyo bayan wani sabani da yayi da yayansa, yayin da yake zargin mahaifinsu da bai wa yayan nasa babban gona.
An tattaro cewa mahaifin nasa, Habu Kuppe ya zo ne domin yin sulhu a tsakanin ‘yan uwan biyu lokacin da Haruna ya yanke shi a kai da baya da adda, inda a nan take ya fadi ya mutu.
Asali: Legit.ng