Sau 3 Ina Kokarin Kashe Mahaifi Na Don In Gaje Dukiyarsa, Dan Jihar Kano

Sau 3 Ina Kokarin Kashe Mahaifi Na Don In Gaje Dukiyarsa, Dan Jihar Kano

  • An damke wani matashi a unguwar Gadon Kaya dake jihar Kano dake kokarin kashe mahaifinsa
  • Matashin ya bayyana cewa ya dade yana son kashe mahaifinsa saboda ya gaji dukiyarsa da ya tara
  • Hukumar yan sandan jihar Kano ta bayyana shi gaban mutan gari da yan jarida

Kano - Hukumar yan sanda a jihar Kano ta damke wani matashi da bindiga a unguwar Gadon Kaya dake cikin birnin jihar Kano.

Matashin mai shekaru 25 da haihuwa, Nasir Kabir, ya bayyana abinda yake niyyar yi da bindigar.

Kabir ya laburtawa yan sanda cewa sau uku yana kokarin kashe mahaifinsa don ya gaje dukiyarsa kuma yaji dadi kamar yadda abokansa ke yi, rahoton DailyTrust.

Yace ya fara shawaran kashe mahaifin ne lokacin da wani mahaifin abokinsa ya rasu a 2018 kuma ya ga yadda abokin ya samu kudin gado da yawa har ya sayi Babur.

Kara karanta wannan

An Kama Matashi Hassan Kan Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 90 Don Ya Sace Katin ATM Dinsa Na Banki

Kabir
Sau 3 Ina Kokarin Kashe Mahaifi Na Don In Gaje Dukiyarsa, Dan Jihar Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabin da ya yiwa manema labarai yayinda yan sanda suka bayyanashi gaban duniya, Nasir Kabir yace:

"Mahaifi na mutumin kirki ne kuma ina son sa. Kuma yana kula da ni. Amma na yi kokarin kashesa don in gaje kudinsa."
"Na fara tunanin haka ne lokacin da mahaifin abokina ya mutu kuma naga irin makudan kudin da aka bashi. Tun daga lokacin na fara shawaran kashe mahaifina."

Kabir ya cigaba da cewa lokacin da farko da ya gwada kashe mahaifinsa a 2018 yana makarantar sakandare inda yayi amfani da maganin 'bera amma tsohon bai mutu ba.

Yace:

"Daya daga cikin abokaina, Saifullahi Sani, ya kira ni kuma yace min akwai bindigan da zamu iya amfani da shi, amma na sayarwa ne. Sai na karbi bindigar, na zagaya wani waje na harba sama. Sai aka kamani ko karasawa gida ban yi ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel