Almundahanar N200m: Gwamnatin Filato Ta Fara Bincikar Tsofaffin ma'aikatan Hukumar Alhazai
- Gwamnatin jihar Filto, ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike don gano yadda aka yi ma'aikatan hukumar alhazan jihar suka yi zambar naira miliyan 200
- An samu korafe-korafe kan ma'aikatan, wadanda aka gano kudin wasu maniyyata sun salwanta ba tare da sun samu zuwa aikin hajjin ba
- Gwamnatin, ta kuma sha alwashin baiwa hukumar alhazan jhar duk wani goyon baya da take bukata a shirye shiryen aikin hajjin bana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Filato - Gwamnatin jihar Filato, ta kafa wani kwamiti da zai binciki jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar, bisa zargin karkatar da kudaden da wasu mutane suka biya na aikin hajjin bara amma ba su samu zuwa ba.
Gwamnatin ta kuma ce, baya ga wadannan kudaden, akwai wasu munanan ayyuka da gwamnatin ta gano ma'aikatan na yi biyo bayan korafe-korafe da jama'a suka yi a kansu.
Gwamna Caleb Mutfwang, wanda ya kaddamar da ‘yan kwamitin a gidan gwamnati da ke Jos, ya ce ana sa ran kwamitin zai binciki dukkan harkokin kudi na hukumar daga watan Yunin 2015 zuwa Mayu 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Filato ta kafa kwamiti
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar, Arc Samuel Nanchang Jatau ya wakilta ya ce, ana sa ran kwamitin zai mika rahotonsa nan da makonni hudu masu zuwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bukace su da su yi abin da ya dace, ya na mai cewa:
“A matsayinku na ‘yan kwamitin, ku tabbatar da adadin maniyyatan, wadanda suka dauki nauyin kansu da kuma wadanda su ke karkashin gwamnati tare da bayar da cikakkun bayanai game da bayanan bankunan su.”
Za mu yi binciken kwakwaf kan zargin rashawar N200m - Hon. Kanam
Gwamnan ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa za ta baiwa hukumar alhazai ta jihar Filato goyon baya, a shirye-shiryenta na gudanar da aikin Hajjin bana a jihar
Ya kuma bukace su da su yi aiki mai inganci tare da bayar da shawarwarin da suka dace.
Da yake mayar da martani, shugaban kwamitin, Hon Abubakar Kanam a madadin kwamitin, ya ce za su yi duk mai yiwuwa don yin adalci tare da tabbatar da yin binciken kwakwaf kan ma'aikatan da ake zargin.
An kara kudin aikin Hajji na shekarar 2023
Hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama guda huɗu na ƙasar nan, sun buƙaci da a ƙara kuɗin hajjin bana na shekarar 2023, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hass an, ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sun buƙaci da a ƙara kuɗin da $250, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Asali: Legit.ng