Hajji 2022: NAHCON Ta Bayyana Kudaden Kujerun Hajjin Bana, Jihohin Borno Da Adamawa Sun Samu Rangwame

Hajji 2022: NAHCON Ta Bayyana Kudaden Kujerun Hajjin Bana, Jihohin Borno Da Adamawa Sun Samu Rangwame

  • Hukumar kula da jin dadin alhazai a Najeriya, NAHCON, ta sanar da kudaden kujerun hajji da maniyatta za su biya a bana
  • NAHCON ta ce maniyatta daga arewa za su biya N2,496,815.29 yayin da takwarorinsu na arewa za su biya N2, 449, 607.89
  • Har wa yau, hukumar alhazai din ta ce maniyattan jihohin Adamawa da Borno za su biya N2, 408, 197.89 saboda kusancinsu da Saudiyya

Hukumar kula da jin dadin alhazai, NAHCON, ta sanar da kudaden kujerun hajji na bana. Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta yi la'akari dukkan lamuran da suka shafi aikin hajjin.

Hajiya Fatima Sanda, shugaban sashin hulda da jama'a na hukumar ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan shekara hudu, Kamfanin jiragen saman Najeriya 'Nigeria Air' ya samu lasisin fara aiki

Hajji 2022: NAHCON Ta Bayyana Kudaden Kujerun Hajjin Bana, Jihohin Borno Da Adamawa Sun Samu Rangwame
Hajji 2022: NAHCON Ta Bayyana Kudaden Kujerun Hajjin Bana. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kudin maniyyata daga sassan Najeriya daban-daban

"Maniyatta daga kudancin Najeriya za su biya N2,496,815.29 yayin da takwarorinsu na arewa za su biya N2, 449, 607.89.
"Maniyattan jihohin Adamawa da Borno za su biya N2, 408, 197.89 saboda kusancinsu da Saudiyya. Kudin jirgin shine babban dalilin samun banbanci a kudin hajjin.
"Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya sanar da hakan a ranar 4 ga watan Yuni yayin taron shugabannin yan kwamitin hukumar kula da jin dadin maniyatta a hedkwatan NAHCON."

Bayan sanawar, dukkan hukumomin kula da jin dadin maniyatta na jihohi sun yaba wa shugabannin hukumar saboda tabbatar da cewa kudin bai haura Naira miliyan 2.5 ba duk da kallubalen da ake fama da shi.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel