Kano: Matashin Dan Kasuwa Ya Rataye Kansa Har Lahira, An Bayyana Dalili
- An shiga jimamin rashin wani matashin ɗan kasuwa a jihar Kano bayan ya rataye kansa har lahira
- Matashin ɗan kasuwar dai ya rataye kansa ne bayan damuwa ta yi masa yawa saboda damfararsa kuɗaɗensa da aka yi
- Ɗan uwan matashin ya bayyana cewa an cinye masa N400,000 waɗanda ya ranta domin siyan wasu kaya, wanda hakan ya sanya shi cikin damuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - An shiga jimami a jihar Kano bayan an yi kaciɓus da gawar wani matashin ɗan kasuwa mai shekara 35 da ake zargin ya halaka kansa a Kano.
Matashin dai ana zargin ya rataye kansa ne a wani ɗaki da ke Unguwar Sharada a birnin Kano, rahoton Aminiya ya tabbatar.
A gawar matashin da aka gano, an ga wata wasiƙa inda ya rubuta cewa "A yi hakuri. Amma sauran ba sai na bayyana ba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin dai yana zaune ne a tare da ɗan uwansa a gidan da lamarin ya auku a Unguwar Sharada.
Ɗan uwan matashin mai suna Hamisu ya bayyana cewa an gano gawar marigayin ne bayan an je nemo ashana a ɗakinsa domin dafa wa yara abincin safe.
Meyasa matashin ya rataye kansa?
Hamisu ya bayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da ɗan uwansa, amma ya lura akwai wani abu da ke damunsa a cikin ƴan kwanakin nan.
Hamisu ya yi nuni da cewa damuwarsa ta fara ne bayan ya ci bashin N400,000 ya siyo wasu kayan ɗaki a hannun wasu mutane. Mutanen bayan sun kai shi gidan da aka ajiye kayan, sun buƙaci ya dawo wata rana ya ɗauka.
A kalamansa:
"Da ya nemi su ba shi lambar wayarsu, sai suka ce tun da ya ga gidan zai iya dawowa kowane lokaci, amma da ya koma bai samu gidan ba."
“Abin da ya sanya shi cikin damuwa kenan saboda kuɗin rancensu ya yi kuma mai su ya taso shi a gaba a ba shi kuɗinsa."
Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba a samu wani ƙarin bayani ba daga rundunar ƴan sandan jihar Kano kan lamarin.
Matashi Ya Rataye Ƙansa a Jigawa
A wani labarin kuma, wani matashi ya yanke shawarar rataye kansa saboda an ƙi amince masa ya auri wacce zuciyarsa ke so.
Sai dai, matashin da sauran kwanansa a duniya domin ratayar ba ta kai ga ajalinsa ba, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng