Kuruciya: Matashi ya rataye kansa saboda an ki amincewa ya auri masoyiyarsa a Jigawa

Kuruciya: Matashi ya rataye kansa saboda an ki amincewa ya auri masoyiyarsa a Jigawa

- Wani matashi ya a yanke hukuncin kashe kansa ta hanyar rataya don an hana shi auren wadda ya ke so

- Wannan al'amari ya faru ne a garin Tudun Guru a karamar Hukumar Hadejia na Jihar Jigawa

- Anyi sa'a matashin bai mutu ba sakamokon ratayar kuma an garzaya dashi asibiti don yi masa magani

Matashi ya rataye kansa saboda an han shi auren masoyiyar sa a Jigawa
Matashi ya rataye kansa saboda an han shi auren masoyiyar sa a Jigawa

Wani Matashi mai Suna Inuwa Muhammad mazaunin unguwar Tudun Guru mazabar 'yan Koli a karamar hukumar Hadejia dake jihar Jigawa ya rataye kansa saboda an hana shi auren budurwarsa kamar yadda kafar yadda shafin sada zumunta na rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: Dokar Hana Kiwo: Gwamnatin Jihar Binuwai za tayi gwanjon dabobin da ta kama

Kamar yadda majiyar Legit.ng ta samo labarin daga wani Malam Aji Kima a garin na Hadejia, anyi sa'a ratayar ba tayi sanadiyar mutuwar matashin ba ba kuma a halin yanzu haka yana asibiti inda ya ke cigaba da karbar magani.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da matasan garin Hadejia ke yunkurin kashe kansu ba a dalinin soyaya, ko da makon da da ya gabata ma wani matashi mai suna Umar Muhammad ya rataye kansa saboda an hana shi auren masoyiyarsa.

A wata labarin kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoto inda gwamnatin jihar Benuwai ta ce za ta fara gwanjon dabobin da ta kwace daga makiyayan da aka samu suna karya dokar hana kiwo a jihar idan basu biya tarar da aka yanke musu ba don karban dabobin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: