Wani bawan Allah ya rataye kansa a jihar Nasarawa

Wani bawan Allah ya rataye kansa a jihar Nasarawa

Wani matashi mai shekaru 30 mai suna James Samuel, ya kashe kansa ta hanyar rataya a wani daji da ke makarantar sakandiren gwamnati da ke Gurku, karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

Mamacin dan asalin kabilar Tiv ne daga jihar Binuwai. Ya kashe kansa ne a daren Juma'a kamar yadda jaridar The Nation ta tabbatar.

Wani mazaunin yankin ne ya gano gawar mamacin. Mutumin dan sanda ne da ke aiki a Abuja kuma ya kai rahoto ga ofishin 'yan sanda da ke Gurku.

Dan sandan ya samu hoton mamacin yana karami da mahaifiyarsa a wurin da ya kashe kansa amma babu wata takardar wasiyya.

Wani bawan Allah ya rataye kansa a jihar Nasarawa
Wani bawan Allah ya rataye kansa a jihar Nasarawa Hoto: The Nation
Asali: UGC

An sauke gawar marigayi James Samuel a kan idon 'yan sanda tare da mika ta asibiti.

Samuel, wanda shine shugaban Tiv a Gurku kuma mahaifin mamacin, ya shiga matukar tashin hankali tare da 'yan uwan mamacin.

Kamar yadda yace, "Marigayin da na ya halarci makarantar sakandiren da ke Gurku. Manomi ne, yana walda da kuma kida.

"Sananne ne a cikin tsararrakinsa. Dan kabilar Tiv ne amma yana jin yaren Gbagyi, Jaba, Hausa da Gwandara.

"Na gano cewa wannan ne karon farko da aka samu wani ya kashe kansa a kasar Gurku kuma babban abun takaici ne," yace.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: El-Rufai ya sanar da mutuwar wani babban mutum a jihar Kaduna

Sarkin Gurku, Alhaji Jibrin Waziri wanda ya yi jawabi ta bakin hadiminsa, ya ce Madakin Gurku, Zubairu Adamu ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya je har wurin da abun ya faru.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani aure mai shekaru takwas ya kare a tashin hankali da rashin dadi a yankin Zumbagwe da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

Ana zargin Janet Ekpe mai shekaru 33 da saka wa mijinta guba a abinci bayan ta zarge sa da soyayya da babbar kawar ta. Ta zuba ido har ya mutu a gaban ta.

Bayan zargin Sunday Ekpe da soyayya da kawarta, ta zarge sa da kaurace mata amma yana gamsar da babbar kawar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng