Wani ya mutum ya rataye kansa bayan ya kashe matarsa da dansa

Wani ya mutum ya rataye kansa bayan ya kashe matarsa da dansa

-Wani mutum ya aika da matarsa da dansa zuwa lahira inda ya rataye kansa a karshe sakamakon zarginta da yake da cin amanarsa.

-Wannan mutum a lokuta da dama ya sha furta cewa dansa da ya kashe ba dan cikinsa bane, ma'ana matarsa ta ha'ince shi.

Charles Enifa mai sana’ar tukin adaidaita sahu ya yi amfani da wuka wurin kashe matarsa da dansa daga nan kuma ya zarce zuwa rataye kansa saboda zargin cin amana dake tsakaninsu.

Wannan abu dai ya auku ne a ranar Alhamis a gida mai lamba I2 Obafemi Eruja street dake shiyar Aga Ikorodu ta jihar Legas.

Wani ya mutum ya rataye kansa bayan ya kashe matarsa da dansa
Wani ya mutum ya rataye kansa bayan ya kashe matarsa da dansa
Asali: UGC

KU KARANTA:‘Yan sanda sun kama soja hudu da wasu mutane 84 akan zargin aikata fashi da makami

An samu gawarwakinsu da misalin karfe 5 na asubah yayin da manyan yaransu Success da Favour suka bude kofar dakin da abin ya faru sai ihu suka fasa domin kiran makwabtansu.

Da dama daga cikin makwabtansu sun yi hijira sun bar wurin zaman nasu sakamakon jin wannan mumunan labari.

Duk da cewa ba’a san hakikanin dalilin kisan ba, sai dai mutanen da suka san iyalan sun bayyana cewa mutumin ya sha furta cewa shi fa yaron da ya kashe ba dan cikinsa bane.

Jamiu Odukoya wanda shine mai gidan da mutanen ke haya a ciki yace, rikici tsakanin ma’auratan ya kai shekara biyu yanzu. Kullum mijin bai da magana sai cewa ba fa shi bane uban yaron da ya kashe.

Yace “ Ni ba mazaunin gidan bane, da safiyar Juma’a aka kirani cewa in zo wani abu ya faru da misalin karfe 10 na safe. Kan nazo sai da na garzaya ofishin ‘yan sanda aka ce dani sun riga sun isa gidan.

“ Da isowata gidan sai na samu labarin cewa wani cikin yan haya ya kashe matarsa da dansa saboda zargin cin amana. Sun dade suna samun wannan matsalar a dalilin hakan ma har shawara an bashi cewa ya rabu da matar tunda yana zarginta amma yaki.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng