Kotu Ta Ci Tarar IGP da Rundunar ’Yan Sanda Naira Miliyan 200 Kan Garkame Matar Aure
- Kotu ta ci tarar babban sufetan rundunar 'yan sanda, da wasu, naira miliyan 200, kan tsare wata matar aure da suka yi tare da karbar mata kudi
- A watan Maris ne 'yan sanda suka kama wacce ta shigar da karar, biyo bayan kudin da ta tura zuwa kasar Spain, wanda hukumar kasar ke zargin na sata ne
- Sai dai, bayan zaman da kotun ta yi, mai shari'ar ya ce rundunar 'yan sanda ba ta da hurumin kwace kudi daga hannun matar, kuma sun tauye hakkin dan Adam
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Uyo, jihar Akwa Ibom - Wata babbar kotun jihar Akwa Ibom dake da zama a Uyo babban birnin jihar, ta ci tarar babban sufetan ‘yan sanda (IGP) da wasu mutane biyar da suka hada da hukumar ‘yan sanda (PSC).
Kotun ta umurce su da su biya wata matar aure a Uyo mai suna Peace Ekom Robert kudi naira miliyan 200.
Alkalin kotun, Mai shari’a Ntong Ntong, ya ba da umarnin ne a ranar Talata a wani hukunci da ya yanke kan shari’ar tauye hakkokin bil’adama da mai shigar da karar ya gabatar a gaban kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da yasa aka kama Peace Ekom Robert
Bayanin shari’ar ya nuna cewa, a watan Maris na wannan shekara, Ifenyinwa Anthonia Olua, ta tuntubi mai karar, Peace Ekom Robert, don ta hada ta da wani a turai da zai iya siyan kudin Yuro ya biya ta da naira.
Matar ta tura yuro 55,000, kwatankwacin naira miliyan 42.9 zuwa asusun wani dan Spain, wanda shi kuma ya kai rahoto ga hukumomin kasar, wadanda suka sanya takunkumi kan asusun.
Bisa zargin kudin na iya zama na sata, su kuma rundunar 'yan sanda, bayan samun rahoto, suka kama wacce ta shigar da karar.
Peace Robert ta shigar da IGP kara tare da wasu
Wadanda aka shigar da karar sun hada da babban sufetan 'yan sanda, kwamishinan da ke kula da harkokin sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Abuja, Mista Babazango Ibrahim.
Akwai kuma karin DSP Yusuf Dauda na sashin yaki da kisan kai, Alagbon a Legas; Sifeta Celestina Ugbaja ta sashin ayyukan damfara na musamman na runduanr da ke Ikoyi, Legas da kuma hukumar ‘yan sanda.
Hukuncin da kotu ta yanke
A cikin hukuncin da ya yanke, mai shari'a Ntong Ntong, ya ce:
"Rundunar 'yan sanda sun dauki doka a hannunsu, wanda ya saba da kundin mulkin kasar na 1999, tare da kin mutunta kotu, da wulakanta ofishin shugaban kasa.
"Don haka, kotu na umurtar wadanda ake karar, su mayar da naira miliyan 15 da aka karba daga hannun wacce ta shigar da karar, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci na karshe."
Asali: Legit.ng