Yan Sanda Sun Kashe Fitaccen Mai Garkuwa da Mutane a Katsina

Yan Sanda Sun Kashe Fitaccen Mai Garkuwa da Mutane a Katsina

  • Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kashe wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, dan asalin kauyen Unguwar Tsamiya, da ke jihar Katsina
  • An kashe dan ta'addan ne a wani samame da rundunar ta kai wata gona da tawagar dan ta'addan su ka farmaka, inda aka yi musayar wuta
  • Rundunar ta kuma kwato harsasai 185 ma su tsawon 7.62mm, alburusai 90 ma su tsawon 5.56mm, da kumaalburusan AK-47 guda 13 da aka boye a cikin buhu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Faskari, jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta kashe wani fitaccen mai garkuwa da mutane, Nazifi Ibrahim, mai shekaru 22, a kauyen Unguwar Tsamiya da ke karamar hukumar Faskari.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kama wani da kokon kan mutum sabon yanka a Ibadan, hotuna sun bayyana

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Aliyu, ya fitar tare da raba wa manema labarai a ranar Asabar, a Katsina.

Jami'an 'yan sanda
Rundunar 'yan sanda ta yi musayar wuta da 'yan bindigar, kafin daga bisani ta kashe mai garkuwa da mutanen Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

ASP Aliyu ya kara da cewa ‘yan sandan sun kuma kwato wasu tarin alburusai, yayin da su ka kai samamen, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“A ranar 11 ga Nuwamba, 2023, da misalin karfe 03:30 na safe, bisa ga bayanan da rundunar ta samu, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai irin su AK 47, sun kai farmaki wata gona da ke bayan kauyen Yankara."
"Bayan samun rahoton, DPO na Faskari ya tattara tawagar hadin gwiwa na jami'an 'yan sanda, 'yan banga, da jami'an tsaron 'Security Watch Corps', zuwa wurin."

An kashe Nazifi Ibrahim - Rundunar 'yan sanda

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Ya ce, masu garkuwa da mutanen, da suka lura da zuwan tawagar hadin guiwar jami'an tsaron, sai suka bude wuta.

A cewarsa, rundunar hadin guiwar, sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan yin watsi da shirin nasu, suka ranta a na kare zuwa cikin daji.

“A yayin da su ke binciken wurin da lamarin ya faru, ‘yan sanda sun gano gawar wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, da harsasai 185 ma su tsawon 7.62mm, alburusai 90 ma su tsawon 5.56mm. M193 kirar 06, da kuma kwankwan alburusan AK-47 guda 13 da aka boye a cikin buhu."
“Daga baya an gano gawar wanda ake zargin, mai garkuwa da mutane ne, mai suna Nazifi Ibrahim, shekaru 22, dan asalin kauyen Unguwar Tsamiya, karamar hukumar Faskari.”

- A cewar ASP Aliyu.

An jinjina wa kokarin 'yan sanda

Aliyu ya kuma bayyana cewa, rundunar na ci gaba da bincike don kamo sauran 'yan bindigar da su ka gudu.

Kara karanta wannan

Umar Ka'oje: Farfesan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan 1 da aka tura masa bisa kuskure

Ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aliyu Abubakar-Musa, ya yabawa dakarun ‘yan sandan tare da sauran jami'an hadin kai da suka kai samamen, saboda irin jarumtar da su ka nuna.

Yan sanda sun dakile harin ta'addanci a Katsina

A wani labarin da Legit Hausa ta kawo maku, kun ji yadda jami'an ƴan sanda a jihar Katsina sun daƙile harin yan ta'adda a kauyen Korogo, cikin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Jami'an yan sandan sun halaka dan ta'adda ɗaya a yayin artabun da suka yi da yan ta'addan, cewar rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel