Ofishin Matar Shugaban Kasa: Aisha Buhari Ta Mika Mulki Ga Remi Tinubu

Ofishin Matar Shugaban Kasa: Aisha Buhari Ta Mika Mulki Ga Remi Tinubu

  • Gabannin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu, Aisha Buhari ta mika kujerarta ga Remi Tinubu
  • Aisha ta mika muhimman takardu na ofishin matar shugaban kasa ga matar shugaban kasa mai jiran gado
  • Asiwaju Bola Tinubu zai karbi mulki a matsayin shugaban kasa daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari nan da kwanaki hudu

Matar shugaban kasar Najeriya mai barin gado, Hajiya Aisha Buhari, ta mika mulki ga matar shugaban kasa mai jiran gado, Oluremi Tinubu.

A ranar 29 ga watan Mayu ne wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai cika inda zai mika mulki ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu.

Aisha Buhari da Remi Tinubu
Ofishin Matar Shugaban Kasa: Aisha Buhari Ta Mika Mulki Ga Remi Tinubu Hoto: Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa an yi bikin mika mulkin ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda Aisha ta mikawa Remi nauyin da ya rataya kan kujerar sannan ta mika mata muhimman takardu domin su yi mata jagora.

Kara karanta wannan

Mataimakin Tinubu Ya Bayyana Wanda Ya Fi Cancanta da Shugabancin Majalisar Dattawa Ta 10

Aisha Buhari ta mika kambun jagorancin kungiyar matan shugabannin Afrika ga Remi Tinubu

Ta kuma mika tambarin wanzar da zaman lafiya na matan shugabannin kasar Afrika ga magajiyarta, wacce a yanzu ita ce za ta zama babbar mai masaukin bakin dukkanin matan shugabannin Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewar aikin matar shugaban kasa baya kundin tsarin mulki, Uwargidar Buhari ta nuna jin dadinta kan damar da aka bata na gudanar da ayyukan taimakon jama'a da kuma hadin gwiwa da kungiyoyin agaji a tsawon shekaru takwas da ta yi a ofis.

Ta ce:

"Kamar yadda kuka sani aikin matar shugaban kasa baya bisa kundin tsarin mulki, amma mun ci moriyar karamcin yan kasa wajen aiwatar da wasu muhimman abubuwa kamar aikin agaji.
"Mun yi hadaka da kungiyoyi masu zaman kansu da dama domin taimakon al'ummarmu, kuma na ji dadin wannan aikin alkhairi tsawon shekaru takwas da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

"Don haka, na shirya mika mulki, don kawai na yi maki jagora, da ganin kungiyoyin agaji da muka yi aiki da su."

A martanin ta, Misis Tinubu ta nuna godiyarta ga uwargidan shugaban kasar. Ta bayyana ta a matsayin jagora ta gari. Ta kuma yaba mata kan yadda ta gudanar da wasu abubuwa, rahoton Punch.

DSS ta bankado shirin da wasu bata gari ke yi na hargitsa bikin rantsarwa

A wani labarin, hukumar DSS ta bayyana cewa tana sane da shirin wasu marasa kishin kasa na son kawo cikas ga bikin rantsarwa da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu a fadin kasar.

DSS ta sha alwashin yin maganin duk wanda ya yi kokarin kawo tangarda ga kokarinsu na son tabbatar da ganin an yi bikin cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel