Yan Bindiga Sun Cinnawa Gonaki Wuta a Neja, Sun Saka Harajin Miliyan 30, Sun Bar Wasika

Yan Bindiga Sun Cinnawa Gonaki Wuta a Neja, Sun Saka Harajin Miliyan 30, Sun Bar Wasika

  • Wasu 'yan bindiga sun ajiye wa manoman Kontagora wasika a gonakinsu, inda suka bukaci kowanne manomi ya biya wa gonarsa harajin naira miliyan 30
  • A cewar wani rahoto, 'yan bindigar sun yi barazanar kai farmaki, tare da kone dukkanin gonakin, ma damar manoman ba su biya harajin da suka sanya masu ba
  • Domin buga misali kan hakan, 'yan bindigar, sun fara cinna wuta a wasu gonaki, don ya zama izina ga sauran manoman da abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wasu ‘yan bindiga sun kona sama da gonaki 20 na masara, waken suya da kuma dawa a wajen garin Kontagora, shelkwatar karamar hukumar Kontagora ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ba da wa’adin kwana 7 ga iyalan mutane 19 da suka sace a Kaduna

Daya daga cikin manoman da lamarin ya shafa ya tabbatar wa City & Crime ta wayar tarho cewa ‘yan fashin sun kuma ajiye musu sako a gonakin kowannensu.

Manoma
Yan bindiga sun sanya wa manoman harajin N30m kowanne, da barazanar kona gonakinsu Hoto: K. Stefanova/USAID
Asali: UGC

A jikin sakon, 'yan bindigar sun nemi kowanne manomi ya biya harajin maira miliyan 30 ko kuma su ci gaba da kai musu hari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bidigar sun yi wa manoman yankin barazana

Ya ce shi bai kira lambar da 'yan bindigar suka bari ba amma wadanda suka kira lambar sun shaida masa cewa 'yan bindigar sun tabbatar musu da cewa sune suka kona amfanin gonakin.

Sannan, sun yi musu barazana da cewa za su yi maganin kowannensu idan har suka kasa biyan harajin da suka dora musu.

Manomin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda gudun barazana, ya roki gwamnatin tarayya da ta jihohi da su nemo hanyar magance hare-haren da ake kaiwa manoma.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da suka sace mutane a kauyen Abuja sun bayyana kudin fansa Da suke nema a biya

Manoma na biyan 'yan bindiga kudi a Kaduna

A jihar Kaduna kuwa, lamarin rashin tsaro ya kai yanayin da mutane su na cire kudi daga aljihunsu, suna mikawa ‘yan bindiga.

Abin da ya sa hakan ta ke faruwa kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto shi ne, mutane na so a cire kayan amfani daga gonaki.

‘Yan bindigan da su ka addabi kauyukan Giwa suna tursasawa manoma biyan kudi idan suna sha’awar girbe abin da su ka noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.