Yajin Aikin NLC Ya Gamu da Babban Cikas a Jihar Ƙaduna Yayin da Ma'aikata Suka Rabu Gida Biyu
- An samu rabuwar kai a jihar Kaduna, wasu ma'aikata sun shiga yajin aiki wasu kuma sun fita wurin aiki kamar yadda suka saba
- A cewar shugaban NLC na jihar, hakan ta faru ne saboda sanarwan ba ta zo musu a kan lokaci ba amma zasu tabbatar da an bi umarni
- Ma'aikata sun fita aiki a sakateriyar jiha, bankuna sun buɗe kamar yadda suka saba, sai dai an rufe kamfanin wutar lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Yajin aikin sai baba-ta-gani da manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC suka shiga bai karɓu yadda ya kamata ba a jihar Ƙaduna.
Kamar tadda jaridar Punch ta tattaro, da yawan ma'aikata a jihar Kaduna sun ci gaba da harkokinsu na aiki kamar yadda aka saba yau da kullum ranar Talata.
Ma'aikata sun bayyana shiga yajin aiki a faɗin Najeriya daga ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023 sakamakon cin mutuncin da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin wuta ya bi sahun shiga yajin aiki
Bayanai sun nuna an rufe hedkwatar kamfanin raba wutar lantarki da ke layin Banki a titin Ahmadu Bello Way a cikin kwaryar birnin Kaduna, an hana ma'aikata da kwastomomi su shiga.
Sakataren tsare-tsare na NUEE reshen Arewa maso Yamma, Bukat Barde, ya ce abin da aka yi wa shugaban NLC cin mutuncin ma'aikata ne kuma bai kamata a bari ya wuce haka nan ba.
Ya ce:
"Ba zamu bar wannan wannan cin zarafin ya wuce haka nan ba, domin wannan cin zarafi ne ga kafatanin ma'aikata a ƙasar nan. Zamu ci gaba da yajin aiki har sai gwamnati ta biya bukatun NLC."
An tattaro cewa ba a bar ma'aikata da kwastomomin kamfanin wutar lantarki sun shiga harabar kamfanin ba sabida yajin aikin.
Ma'aikatan gwamnati sun je wurin aiki
Haka zalika an bude sakatariyar jihar da ke kan titin Independence ga ma'aikata kuma sun fito sun ci gaba da gudanar da ayyukansu.
"Ba a bamu umarnin shiga yajin aiki ba," in ji wani ma'aikaci wanda ya nemi a sakaya bayanansa.
Bankuna sun buɗe sun ci gaba da harkokinsu sannan gidajen mai sun buɗe suna gudanr da harkokinsu na kasuwanci yadda aka saba, The Cable ta ruwaito.
Meyasa haka ta faru a Kaduna?
Da aka tuntubi shugaban NLC a jihar, Kwamared Ayuba Suleiman ya ce:
"Hakan ta faru ne saboda sanarwan shiga yajin aikin ta zo mana da daddare kuma akwai buƙatar kiran taro da kafa kwamitin da zai tabbatar da an bi umarnin"
"Yanzu haka taron na gudana kuma da zaran mun kammala zamu tabbatar da yajin aikin ya karaɗe ko ina."
Wani Malamin makaranta a cikin garin Kaduna, Nura Aliyu, mazaunin Unguwar Mu'azu, ya shaida Legit Hausa cewa ya je makaranta kuma an yi karatu a ranar da aka tafi yajin aiki.
Ya ce ya samu labarin tafiya yajin aikin a kafafen yaɗa labarai amma batun bai zo makarantarsu a hukumance ba.
"Gaskiya mun je makaranta, sai dai wasu ɗalibai har da malamai ba su samu zuwa ba, sun ɗauka an tafi yajin aikin. Daga baya dai lokacin tashi bai yi ba, haka shugaba ya ce a sallami kowa."
Ya kara da cewa daga baya kuma suka samu labarin ƙungiyar kwadagon ta janye yajin aikin gaba ɗaya.
Ma'aikata a Jihar Delta Sun Kauracewa Wurin Aiki
A wani rahoton kuma Ayyuka sun tsaya cak a Sakateriyar tarayya da ta jiha da ke Asaba, babban birnin jihar Delta biyo bayan umarnin NLC na shiga yajin aiki.
Ma'aikatan jihar ba su fita wuraren ayyukansu ba, kuma an ga mambobin NLC sun je sun garƙame ma'aikatun tun ƙarfe 8:00 na safiya.
Asali: Legit.ng